A yayin da al’ummar Sinawa ke shirye-shiryen bikin bazara wato Spring Festival a Turance, bikin gargajiya mafi kasaita ga Sinawa, dake alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar, haka ma al’ummar duniya ke jiran wannan kasaitaccen biki mai tsawon tarihin da ya kai kimanin shekaru 4000, wanda ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 2024. Rahotanni na nuna cewa, yawan zirga-zirgar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye ta jiragen kasa a kasar Sin a ranar 5 ga wata kadai, ya kai miliyan 12 da dubu 198. Kana a ranar 6 ga wata, ana hasashen adadin zai karu, inda ake zaton zai kai miliyan 12 da dubu 900, wannan ya sa aka kara samar da jiragen kasa 1789. A halin yanzu, zirga-zirga ta jiragen kasa a dukkan kasar Sin na gudana yadda ya kamata, kuma harkokin zirga-zirgar jiragen kasa na komawa kamar yadda aka saba a tashoshin jiragen kasa da matsalar yanayi ta shafa.
Lokacin bulaguro na bikin bazara na kasar Sin na bana yana daukar kwanaki 40 daga ranar 26 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Maris. Hukumomin zirga-zirga da sufuri na kasar Sin sun yi hasashen cewa, mutane kimanin biliyan 9 ne za su yi zirga-zirga tsakanin yankuna a fadin kasar a cikin wannan lokaci, wanda ya kusan ninka adadin a shekarar 2023. Wannan a cewar masu fashin baki, ya kara nuna yadda al’ummar Sinawa ke daukar al’adunsu na gargajiya da matukar muhimmanci, duk da ci gaban zamani, hakan bai sanya su watsi da al’adunsu ba.
- Kasar Sin Ta Taya Nangolo Mbumba Murnar Zama Sabon Shugaban Namibia
- Li Qiang Ya Tattauna Da Kwararrun ‘Yan Kasashen Waje Dake Kasar Sin
Babbar manufar wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa, ba ta sauya ba a tsawon shekaru masu yawa, wato haduwa da iyalai bayan tsawon shekara, don murnar shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.
A kowace shekara, Sinawa na amfani da dabbobi 12 domin wakiltar kowace shekara, a bana sabuwar shekarar gargajiya ta Sin shekara ce ta dabbar Loong. Sauran dabbobin dake alamta kowace shekara sun hada da Bera, da Saniya, da Damisa, da Zomo, da Maciji, da Doki, da Rago, da Biri, da Kaji da Kare da kuma Alade.
Saboda tasiri da muhimmancin wannan biki, yanzu haka an nuna dandanon shagulgulan bikin na bana a kasashe da dama na duniya, da suka hada da Brazil da Rasha, da Najeriya da Masar, da Amurka da Habasha da Kenya da sauransu. Kuma idan ba a manta ba a karshen shekarar da ta gabata ce, babban taron MDD karo na 78 ya zartas da kudurin sanya bikin bazara, a matsayin lokacin hutu na MDD, baya ga kusan kasashe 20 na duniya da suka ayyana bikin bazara a matsayin lokacin hutu a hukumance, yayin da kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya ke murnar bikin bazara ta hanyoyi daban-daban.
Babban sako ga daukacin al’ummar duniya shi ne, kowa ya rike al’adarsa da muhimmancin gaske, domin kayan aro ba ya rufe katara. (Ibrahim Yaya)