Akwai wani kasaitaccen bikin baje kolin kayayyaki, wanda aka kafa shi ba domin sayar da hajoji zuwa kasashen ketare ba, maimakon haka ana ba da taimako ga ‘yan kasuwar kasashen waje don su samu damar sayar da karin kayayyakinsu. Wannan biki shi ne bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga kasashe daban daban, ko kuma CIIE a takaice, wanda a kan gudanar da shi a watan Nuwamban kowace shekara a birnin Shanghai na kasar Sin.
Bayan wasu kwanaki, wato a tsakanin ranar 5 da ta 10 ga watan Nuwamban bana, za a shirya bikin CIIE karo na 9. Yanzu haka dimbin kasashe dake nahiyar Afirka suna mai da cikakken hankali kan wannan biki da ke tafe, inda suke sa ran yin amfani da wannan dama wajen neman sayar da karin kayayyaki a kasuwannin kasar Sin. An ce, a wajen bikin CIIE na wannan karo, kasar Gabon za ta kafa rumfarta a karon farko, kana kasar Kodibwa ita ma za ta sanya dimbin kamfanoninta halartar bikin tare, inda za su yi baje kolin kayayyaki kamarsu koko, da gahawa, da kyashu, da goro, da kuma kayan masaku. Yayin da a nata bangare, kasar Zimbabwe take dogaro kan tsohuwar sana’arta ta sarrafa fata, inda take neman sayar da karin kayayyakin fata masu daraja ga Sinawa, duk bisa amfani da damar bikin CIIE na wannan karo.
Tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yafe wa kasashe 53 da ke nahiyar Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da ita harajin fito.
Baya ga wannan batu, dimbin bukukuwan kasuwanci irinsu bikin Canton Fair da bikin CIIE da kasar Sin take shiryawa, sun sa kasashen Afirka samun damar sayar da karin kayayyaki zuwa kasar Sin, tare da bai wa jama’ar kasashen karin kudin shiga. Misali, yawan ganyen shayi da kasar Kenya ta fitar zuwa kasar Sin ya karu daga kilo miliyan 2 a shekarun baya, zuwa kilo miliyan 12.4 a shekarar 2025, ban da haka ana sa ran ganin adadin ya kai kimanin kilo miliyan 20 a shekarar 2026.
Sa’an nan a nasa bangare, ministan kula da aikin kiwon dabbobi na kasar Madagascar, Riana Randrianomenjanahary, ya ce, tun bayan da aka fara nuna naman tunkiya na kasar a bikin CIIE na shekarar 2024, kasar tana ta fitar da karin naman tunkiya zuwa kasar Sin, tare da samar da dimbin guraben aikin yi a kauyukan kasar ta Madagascar, lamarin da ya sanya magidanta a kalla 3000 samun ingantuwar rayuwa.
Kila za ka yi mamakin dalilin da ya sa kasar Sin shirya bikin CIIE. A hakika kasar ta yi haka ne don neman cika alkawarinta na tabbatar da moriyar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki yayin da take hulda da sauran kasashe. A bangaren kasar Sin, ta hanyar shirya bikin CIIE da shigar da karin kayayyaki daga ketare, kasar tana iya biyan bukatun masu sayayya dake cikin gida na sayen karin kayayyaki masu inganci kirar kasashe daban daban.
Ban da haka, ta hanyar shigar da fasahohi da hidimomi da kayayyaki masu inganci, kasar za ta samu damar tilasta wa kamfanonin cikin gida su inganta kansu a kai a kai. Sa’an nan a fannin al’amuran duniya, yadda kasar Sin take shirya bikin CIIE ya sa dimbin kasashe masu tasowa fitar da karin kayayyaki, da more ci gaban tattalin arziki. Kana a bisa wannan tushe ne, kasar Sin ke neman nuna wa mutanen duniya cewa, ba za ta taba rufe kofarta ba, kuma har kullum tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci da na dunkulewar duniya, da adawa da ra’ayin kariyar ciniki da matakin raba-gari.
A nata bangare, kasar Najeriya bisa matsayinta na babbar abokiyar huldar kasar Sin ta biyu a fannin ciniki a nahiyar Afirka, ta halarci dukkan bukukuwan CIIE da suka gudana a baya, kana ta zama kasa babbar bakuwa a bikin CIIE na shekarar 2025. Yanzu dimbin amfanin gona na kasar Najeriya irinsu kyashu, da ridi, da gyada, sun riga sun shiga kasuwannin kasar Sin ta hanyar bikin CIIE. Kana wasu ma’adinanta ma sun ja hankalin baki na mabambantan kasashe, bayan da aka yi baje kolinsu a bikin CIIE. An yi hasashen cewa wasu kasashe da yankuna 162, da kamfanoni 4142 na kasahe daban daban, za su halarci bikin CIIE na wannan karo.
Ta la’akari da yadda kasar Najeriya ta halarci dukkan bukukuwan CIIE da suka gudana a baya, bai kamata ta yi watsi da damammakin masu kyau da bikin na wannan karo zai samar na sayar da karin kayayyaki zuwa kasar Sin, da kulla huldar hadin gwiwa ta fuskar ciniki da karin abokan hulda na kasashe daban daban ba.
A wajen bikin CIIE dake tafe, kamfanonin Najeriya nawa za mu gani? Kana wadanne kayayyaki ne za su yi baje kolinsu? To, za mu samu amsar tambayoyin, a lokacin da aka kaddamar da bikin a ranar 5 ga wata mai zuwa, a birnin Shanghai na kasar Sin. (Bello Wang)













