Ƙungiyar masu dauke da cutar sikila ta jihar Kebbi ta jaddada buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen wayar da kan jama’a kan cutuka hudu masu alaƙa da jini a wajen bikin ranar Sikila ta duniya.
Cutukan da ƙungiyar ke muradin ganin an wayar da jama’a a kai sun haɗa da cutar sikila, domin rage yawaitar mace-mace jama’a.
- Hunturu: Gidauniya Ta Tallafa Wa Masu Larurar Amosanin Jini 300 Rigunan Sanyi A Kaduna
- Yadda Za A Yaki Ciwon Sikila A Nijeriya Daga Tushe – Hajiya Badiyya
Dr. Garba Umar Kangiwa, wani Ƙwararre ne kan cututtuka masu alaƙa da jini a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi, ya bayyana cewa a duk shekara ana haifuwar yara 138,000 masu fama ɗauke da cutar sikila, kashi 25% a ciki ‘yan Nijeriya masu ɗauke da cutar.
Dr. Umar Kangiwa ya bayyana waɗannan alƙaluma yayin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron. Ya ce cikin mutane huɗu na ‘yan Nijeriya mutum ɗaya na ɗauke da cutar sikila.
“Cuta ce ta gado daga iyaye biyu, tana yin tasiri sosai ga ɗaiɗaikun mutane da iyalai da al’umma baki-ɗaya da shafar yanayin tattalin arziki,” Cewar Dr. Kangiwa