Bikin murnar cika shekaru 80 da cimma nasarar babban yakin kare kasa na tsohuwar tarayyar Soviet da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha, ya sake tunatar da al’ummomin duniya game da abubuwan da suka wakana a tarihi. Yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Rasha a daidai wannan lokaci tare da halartar bikin yana da ma’ana mai matukar muhimmanci, wanda ya isar da sakon kasar Sin ga duniya, wato har kullum kasar tana tsayawa tsayin daka a kan kiyaye tsarin duniya, kuma kullum tana daukar nauyin da ke bisa wuyanta na gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Tarihi tamkar madubi ne. A yakin da aka gudanar a tsakanin masu kishin adalci da masu zalunci yau da kimanin shekaru 80 da suka wuce, da Sin da Rasha sun kasance muhimman fagage na yakin a Asiya da kuma Turai, wadanda suka ba da gudummawa mai matukar muhimmanci wajen cimma nasarar yakar ‘yan “Fascist” a duniya. Sai dai har bayan wucewar shekaru 80, ba a kai ga kawo karshen nuna fin karfi a duniya ba, inda ra’ayin kashin kai, da yin fito na fito a tsakanin kasa da kasa ke ci gaba da addabar duniya.
- Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali
- Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU
A kwanakin baya, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da tsai da ranar 8 ga watan Mayun kowace shekara a matsayin “ranar nasarar Amurka”, kuma a cewarsa, “Ko kana so ko ba ka so, sabo da mu ne aka kai ga samun nasarar”, “tankoki da jiragen yaki, da manyan motoci, da jiragen sama, da kuma sojoji na kasar Amurka ne suka ci nasara a kan makiya a shekaru 80 da suka wuce. Idan babu Amurka, to sam sam ba nasarar yakin.” Lallai furucin na shugaba Trump da ya mai da nasarar da kasa da kasa suka samu a matsayin gudummawar da Amurka ita kadai ta bayar, ya sake shaida mana nuna fin karfi da kasar Amurka ta saba yi.
Nasarar yakin duniya na biyu nasara ce ga dukkanin bil Adama, sabanin ta wata kasa daya kadai. Miyagun hasarorin da yakin ya haifar sun bayyana cewa, danniya da zalunci ba hanyar da ta dace ta cudanyar al’ummomin duniya ba ce, kuma nuna karfin soja ba dabara ce ta kiyaye zaman lafiya ba, haka kuma cin nasara daga faduwar wani bangare ba zai kai ga ci gaban dan Adam ba. Za a iya tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam, matukar an yi koyi daga darasin tarihin yakin duniya na biyu, tare da yin watsi da kowane irin ra’ayi na nuna fin karfi.
Kasashen duniya na rungumar adalci a maimakon nuna fin karfi, kuma manufar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam da kasar Sin ta gabatar ta nuna mana hanyar da ta dace ta cudanyar kasashen duniya. Don haka ma, tun bayan da aka gabatar da ita a shekaru 10 da suka wuce, an shigar da ita cikin kudurin MDD, da ma tsarin kungiyar SCO da ta BRICS, lamarin da ya shaida yadda kasa da kasa suka cimma daidaito a kan wannan dabara ta kasar Sin.
Baya ga haka, duniya ta shaida yadda kasar Sin ta yi watsi da mulkin mallaka, da cin nasara daga faduwar wani bangare a yayin da take zamanantar da kanta, har ma ta bude sabon babin hadin gwiwar samun nasarar juna. Daga nasarorin da aka cimma bisa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, zuwa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin da ya samar da dandalin more damammaki ga duniya, kuma daga samar da hidimomin tauraron dan Adam na Beidou ga kasa da kasa, zuwa yadda fasahar Juncao ta samar da moriya ga kasashe sama da 100, kasar Sin ta shaida wa duniya cewa, kasashe masu tasowa suna iya zamantar da kansu ba tare da bin hanyar da kasashen yamma suka bi a baya ba.
Tarihi ya haskaka makomar dan Adam, kuma muna da imanin cewa, Bil’adama zai iya samar wa kansa kyakkyawar makoma muddin ya rike tarihi a zuci, kuma ba za su kai ga cimma nasara a kan kalubalen da ke gabansu ba, har sai sun hada kai da juna. (Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp