Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kamata ya yi manyan sassan nan biyu wato Sin da EU, su ci gaba da bunkasa dangantakarsu bisa turba ta gari, su kuma yi aiki tare wajen ingiza ci gabansu a shekaru 50 masu zuwa.
Xi Jinping ya bayyana haka ne a yau Alhamis, a babban dakin taruwar jamaa dake birnin Beijing, yayin ganawarsa da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen, a wani bangare na taro karo na 25, na tattauna batutuwan da suka shafi alakar Sin da EU. Ya ce, taron sassan biyu ya yi matukar jawo hankulan sassan kasa da kasa.
- Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
- Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
Wata kuriar neman jin raayoyin jamaa da kafar CGTN ta gudanar game da hakan, ta nuna yadda masu bayyana raayoyi 3,895 daga kasashe membobin kungiyar EU 10, sun nuna gamsuwa da nasarorin kasar Sin a fannin zamanantar da kasa, suna masu bayyana karfin gwiwa game da yanayin da ake ciki, da ma makomar alakokin Sin da EU, tare da kira ga kasashen Turai da su hada hannu da Sin, wajen goyon bayan tsarin cudanyar mabambantan sassa.
Cikin raayoyin da aka tattara daga kasashen 10, raayoyi daga bakwai sun nuna gamsuwa da ta kai kaso sama da 50 bisa dari, yayin da matasa yan shekaru 25 zuwa 34 suka bayyana kyakkyawan fata ga dangantakar Sin da EU da kaso 76.1 bisa dari.
Har ila yau, kuriun jin raayin jamaar sun nuna gamsuwa da ci gaban kasar Sin a fannin raya tattalin arziki da fasahohi, inda kaso 86 bisa dari suka bayyana Sin a matsayin kasa mai karfin gaske, kana kaso 73.1 bisa dari suka bayyana kwarin gwiwa ga makomar tattalin arzikin kasar a tsawon lokaci. Sai kuma kaso 78.1 bisa dari na masu bayyana raayin da suka amince da ikon Sin, na gudanar da kirkire-kirkire tun daga tushe, yayin da kaso 81.5 bisa dari suka jinjinawa muhimmiyar gudummawar da fasahohin Sin suka samar ga kasuwannin duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp