A bana ake cika shekaru 10 da fara aiwatarwar yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi. Sakamakon wani bincike da kafar yada labarai ta CGTN, ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta fitar, bisa matsayar masu bayyana ra’ayoyi 33,000 daga kasashen duniya 48, ya nuna galibinsu sun cimma matsaya daya kan batun kula da yanayin duniya cikin gaggawa a tsawon lokaci, kuma manufofin Sin da nasarorin da ta samu yayin da ta shiga harkokin kula da yanayin duniya sun samu matukar yabo.
Binciken ya gano cewa, kashi 90% na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, magance sauyin yanayi yana da matukar muhimmanci. Kashi 76.7% sun yi imanin cewa kasar Sin tana sarrafa fitar da hayaki mai dumama yanayi yadda ya kamata. Kazalika, kashi 73.4% na masu bayyana ra’ayoyin sun amince da tsarin da Sin ke bi wajen gudanar da harkokin kula da yanayi na duniya, kuma suna fatan za ta taka muhimmiyar rawa a nan gaba.
CGTN ce ta gudanar da wannan bincike tare da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta kasar Sin, kuma ta gudanar da binciken ne tsakanin masu bayyana ra’ayoyi a sassan duniya ta hanyar kwalejin nazarin sadarwa ta duniya ta sabon zamani. (Safiyah Ma)














