Cibiyar yaki da yada cututtukan na’ura mai kwakwalwa ta kasar Sin wato CVERC, da dakin gwaje-gwajen fasahohin yaki da cututtukan na’ura mai kwakwalwa ta kasar, gami da kamfanin 360 Digital Security Group, sun fitar da wani rahoto cikin hadin-gwiwa a ranar 15 ga watan Afrilu, inda suka bankado makarkashiyar da wasu hukumomin kasar Amurka suka kulla, ta aiwatar da wani mataki mai suna “Volt Typhoon”, da nufin karfafa ayyukan sa ido a ciki da waje kan harkokin intanet da hukumomin leken asirin Amurka suka yi, ta hanyar hura wutar rikicin dake cewa, wai kasar Sin na haifar da barazanar kai hari kan harkokin intanet.
A yayin wani binciken jin ra’ayin jama’a da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gudanar, kashi 91.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayin su a binciken sun ce in dai gwamnatin Amurka ta ci gaba da sa ido gami da kai hari ta intanet, kwarjininta zai ragu ainun cikin sauri.
- Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Kammala Aikin Shimfida Hanyar Mota A Kasar Comoros
- Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Hungary
Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa, kashin 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayi na ganin cewa, Amurka na amfani da fifikon kimiyya da fasaharta don yin babakere a duniya, yayin da kaso 95.7 bisa dari da suka yi tir da danyen aikin da Amurkar ta yi, na danne sauran kasashe bisa hujjar “tsaron kasa”.
An samo wadannan alkaluma ne daga binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar ta intanet, cikin harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da kuma Rashanci, inda sama da mutane dubu 86 suka jefa kuri’a gami da bayyana ra’ayoyinsu. (Murtala Zhang)