Bana ita ce ta cika shekaru 35 da kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Bunkasa Tattalin Arzikin Yankin Asiya da Pacific da ake wa lakabi da APEC.
A yayin da taron shugabannin kungiyar ta APEC karo na 31 ke karatowa, wani binciken jin ra’ayoyin mutane masu amfani da shafukan intanet da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar ya nuna kashi 86.4 na masu ba da amsa sun yaba wa APEC bisa gagaruman nasarorin da ta samu wajen habaka tattalin arzikin yankin da kuma zurfafa hadin gwiwar tattalin arzikin yankin wanda ya kara daukaka matsayin ’yancin cinikayya da zuba jari.
- Shugaba Xi Jinping Ya Tashi Daga Beijing Don Halartar Taron APEC
- Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Taron Kasashen Larabawa Da Musulunci A Riyadh
Har ila yau, ana ganin wannan ya kara saukaka hada-hada a yankin Asiya da Pacific da kuma dora shi a turbar hadin gwiwar tattalin arzikin yanki mafi kuzarin aiki mai kunshe da karfin samun ci gaba mafi girma a duniya.
Kungiyar APEC ita ce kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yanki na farko da kasar Sin ta shiga ciki daga lokacin da ta fara gyare-gyare da bude kofa.
Shigar kasar Sin cikin APEC ta kasance mai matukar muhimmanci gare ta, ta fuskar zurfafa shiga a dama da ita a harkokin tattalin arzikin duniya. Bugu da kari, ci gaban kasar Sin ya samu tagomashi daga yankin Asiya da Pacific kuma ita ma Sin ta rama biki ta hanyar amfanar da yankin da irin ci gaban da ta samu.
A binciken ra’ayoyin, kashi 95.1 na masu ba da amsa sun nanata cewa kasar Sin tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a matsayin jagora a hadin gwiwar tattalin arzikin APEC, kana suka yaba wa kasar bisa fadada bude kofarta ga kasashen duniya da shiga a dama da ita sosai cikin harkokin APEC da kuma muhimmiyar gudunmawar da take bayarwa ga samun ci gaba da kwanciyar hankalin yankin Asiya da Pacific. (Abdulrazaq Yahuza Jere)