Sakamakon cikar sabuwar gwamnatin Amurka wata guda a kan karagar mulki, kafar yada labarai ta CGTN tare da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta kasar Sin da cibiyar nazarin sadarwa ta kasa da kasa a sabon zamani, sun gudanar da wani bincike na sauraron ra’ayoyin jama’a su 7,586 daga kasashe 38 na duniya.
Binciken ya nuna abubuwan da sabuwar gwamnatin Amurka ta aikata, kamar warware yarjejeniyoyi, da ficewa daga kungiyoyin kasa da kasa, da kuma haifar da takaddamar kasuwanci, sun haifar da damuwa da suka a tsakanin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya. Masu bayyana ra’ayoyin daga kasashen G7 da kuma cikin Amurka sun bayyana ra’ayoyi na tir game da tasirin manufofin sabuwar gwamnati.
- Masu Sana’ar Kamun Kifi Sun Koka Kan Ƙarancin Kuɗaɗen Shiga A Taraba
- INEC Ta Buƙaci Majalisa Ta kirkiro Dokar Hana ‘Yan Siyasa Zuwa Rumfunan Zabe Da Maƙudan Kuɗaɗe
Binciken ya nuna cewa kashi 63.7 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa dabi’ar sabuwar gwamnatin ta Amurka ta sake fara ‘janyewa daga kungiyoyin kasa da kasa’ na da mummunan tasiri a harkokin mulkin duniya. Kason masu bayyan ra’ayoyin da suka fadi haka ya karu zuwa kashi 66.7 daga kasashe kawayen Amurka na asali.
Bugu da kari, kashi 63.3 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa manufar sabuwar gwamnatin Amurka ta ‘Amurka ta zamo a farko’ tana kara lalata tattalin arzikin duniya da ke ja baya cikin hanzari. Kashi 58.4 cikin dari na mutanen kuma suna ganin kariyar cinikayyar Amurka za ta kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasashensu.
Binciken ya hada har da wadanda aka ji ra’ayoyinsu daga kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Birtaniya, Italiya, Australia, Jamus, Faransa, Japan, da Koriya ta Kudu, da kuma wasu daga kasashe masu tasowa kamar Brazil, Afirka ta Kudu, Masar, Malaysia, Chile, Najeriya, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Vietnam. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp