Hukumomi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun sanar da cewa, a bana, za a kara lambunan shakatawa 22, da kananan lambunan shakatawa 50.
Ana sa ran zuwa karshen bana, kaso 89 na mazauna birnin za su samu kananan wuraren shakatawa da tazarar dake tsakaninsu ba za ta zarce mitoci 500.
Yanzu haka, akwai lambunan shakatawa nau’o’i daban-daban da yawansu ya kai 1050, a birnin Beijing. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp