Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa ƙasarsa ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci. Sanarwar ta fito ne a rubutunsa da ya wallafa a shafin X a ranar Lahadi.
“Yau, domin dawo da fata ga zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila, da kuma mafita ta ƙasashe biyu, Biritaniya ta amince da Falasɗinu a hukumance,” in ji shi. Wannan mataki ya biyo bayan gargaɗin da ya yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu a watan Yuli cewa ta daina takura wa al’ummar Gaza ta hanyar yunwa, ko kuma Birtaniya ta ɗauki matakin amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu.
- An Gabatar Da Fim Mai Taken Shen Zhou 13 A Kasar Birtaniya
- Isra’ila Ta Fara Sakin Fursunonin Falasɗinawa 369, Ciki Har Da Waɗanda Aka Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai
A lokacin da ya fitar da sanarwar, Starmer ya karɓi baƙuncin Shugaban Amurka, Donald Trump, a Landan, mako guda kafin taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da za a gudanar a New York. Haka kuma, a ranar Lahadin, Kanada da Ostiraliya sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, bayan da Ireland, Spain da Norway suka yi hakan tun bara.
Masaniyar siyasar Gabas ta Tsakiya daga Jami’ar UCL, Dr Julie Norman, ta ce wannan mataki ba zai sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da Falasɗinu ba saboda yuwuwar Amurka ta yi amfani da ikon toshewa, amma ta bayyana cewa goyon bayan Birtaniya da Faransa zai zama “sauyin ɗabi’a mai ƙarfi” ga Falasɗinu a wani lokaci da rikici ya yi tsanani a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
Ta ƙara da cewa wannan amincewa na iya buɗe ƙofa ga sauye-sauyen diflomasiyya, ciki har da yiwuwar buɗe ofishin jakadanci a Landan, duk da cewa tasirin kai tsaye ga rayuwar al’ummar Falasɗinawa zai ɗauki lokaci kafin a gani a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp