Gwamnatin tarayya ta amince da tsame kananan masana’antu, kamfanoni da manoma daga biyan kebantaccen haraji da nufin rage yawan haraji da ke kan kamfanonin.
Kazalika, gwamnatin ta kuma yi garanbawul ga tsarin harajin da ake kan a da rage yawan harajin ga kamfanoni da kuma aiwatar da manufofi masu rahusa domin kaucewa rugujewar kamfanonin.
- Harajin Da EU Ta Sanyawa Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin, Ita Zai Yi Wa Illa
- EU Na Shirin Kakaba Harajin Wucin Gadi Kan Ababen Hawa Masu Amfani Da Lantarki Kirar Kasar Sin
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyara fasalin haraji, Taiwo Oyedele shi ne ya sanar da hakan a ranar Talata a shafinsa na Tiwita, inda ya kara da cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sabon kebantaccen harajin.
A cewarsa, tsohon kebantaccen haraji da ake amfani da shi da aka aiwatar tun a 1978, cike yake da batutuwan da suka shafi janyo karuwar adadi a yayin hulda na babu gaira babu sabab, janyo karancin masu biyan haraji na tsawon lokaci, rashin adalci, lafta wa kamfanoni kudi sosai da dai sauransu.
Kebantaccen haraji wani hanya ne na tattara kudin shiga na haraji da ya kama daga kaso 5 cikin 100 zuwa 10 cikin 100, ya dangane da irin kasuwancin da za a yi. Ana tattara shi ne zuwa ranar 21 na watan da ke tafe. Rashin biya a kan lokaci ka iya janyo a ci tarar kamfani har naira 25,000 a watan farko da kuma 5,000 kari kan haka a kowace wata da aka kasa cika ka’ida.
Ya ce: “Kebantaccen haraji an gabatar da shi a Nijeriya ne tun 1977 da nufin biyan haraji gabanin gudanar da wasu takaitattun kasuwanci. Tsawon lokaci tsarin na wahalar da kamfanoni da janyo musu matsaloli da dama, sannan ya na kawo musu nakasu wajen biyan faraji.
“A kokarin gwamnati na kyautata biyan haraji, don haka ne aka gabatar da sabon tsarin amsar kebantaccen haraji a Nijeriya da nufin saukaka wa kananan kamfanoni.
“Wadanda aka tsame daga biyan kebantaccen harajin sun hada da kananan masana’antu, kamfanoni da manoma domin rage musu wahalhalun biyan haraji.
“Hakan don saukaka biyan haraji da tafiya daidai da duniya ne aka dauki wannan matakin,” ya shaida.