Ana zargin ’yan ta’addan Boko Haram da kashe manoma da wasu mutane da suka tafi tara itacen girki 15 a yankunan Ala da Musune da ke ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kai wa mutanen harin ne a gonakinsu da yammacin ranar Laraba.
Mutane 18 ne suka je gonakinsu, amma an gano gawarwaki 15, yayin da aka binne su a ranar Alhamis.
Har yanzu ba a san inda sauran mutane uku suke ba.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce jami’an tsaro na ƙoƙarin gano inda mutanen ukun suke.
“Eh, an kai hari Marte. An kashe mutane 15, yayin da wasu suka ɓace. Ana ci gaba da ƙoƙarin gano inda suke,” in ji Daso.
Majiyoyi a yankin sun ce waɗanda aka kashe sun haɗa da matasa, maza masu aure da kuma tsofaffi.
Sun ce an yi musu kwanton bauna ne yayin da suke aikin gona da kuma tara itace.
Wata majiya ta ce an daure wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sannan aka harbe su har lahira.
An kuma ce wasu daga cikin gawarwakin sun lalace sosai.
Daga baya, mutanen yankin sun kwashe gawarwakin daga wajen tare da binne su bisa tanadin addinin Musulunci.
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan.
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su ɗauki matakan gaggawa domin kare al’ummar da ke yankin.














