Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta fara bincike kan damuwar da jama’a suka nuna game da audigar al’ada ta mata da ake amfani da su a Nujeriya.
Hukumar ta ce fara bincike a kan wasu audigar mata da aka yi wa rajista domin gano sinadarai masu illa, ciki har da volatile organic compounds (VOCs).
Wannan bincike ya biyo bayan zarge-zarge da aka dinga yi a kafafen sada zumunta cewa wasu audigar na ɗauke da wasu sinadarai masu cutarwa.
Wasu mata kuma sun bayyana cewa su kan yi fama da ƙaiƙayi, jin zafi, cututtuka da sauye-sauye a yanayin jinin al’ada bayan amfani da wasu nau’o’ikan audigar.
NAFDAC ta ce audigar na cikin kayan da ake sa ido a kansu, kuma dole ne su cika ƙa’idojin inganci da tsaro kafin da kuma bayan yi musus rajista.
Hukumar ta kuma ce tana binciken wata audigar mata da aka shigar mata da ƙorafi a kanta.
An ɗauki samfurinta zuwa ɗakin gwaje-gwaje domin gudanar da bincike, ciki har da binciken ƙwayoyin cuta da kuma gano ko tna haifar da matsalar fata.
NAFDAC ta jaddada cewa samun rahotannin wasu mutane na fuskantar matsala bayan amfani da wata audigar ba yana nufin ba ta da inganci ba, saboda mutane na iya samun bambancin a yadda jikinsu ke amsar saƙo.
Hukumar ta ce za ta dogara ne kan sakamakon binciken kimiyya da gwaje-gwajen ɗakin gwaje-gwaje kafin ta yanke shawarar ko akwai buƙatar ƙara sanya ƙa’idoji, kamar ƙara gwajin VOCs ko taƙaita amfani da wasu sinadarai.
NAFDAC ta tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa za ta ci gaba da sanya ido kan kamfanonin da ke haɗa audigar al’ada ta mata don kare lafiyar jama’a.














