Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby, ya sanar da mutuwar sojojin kasar bakwai sakamakon taka bam da motarsu ta yi a wani yankin kasar da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISIS ke cin karensu ba babbaka.
Shugaba Deby Itno ne, ya tabbatar da mutuwar sojojin, inda ya ce akwai wasu da dama da suka samu raunuka a yankin Tchoukou Telia da ke gabar tekun tafkin Chadi.
- Gwamna Dauda Lawal Ya Gana Da Ministan Ruwa Domin Kammala Ayyukan Ruwa A Zamfara
- Wang Yi Ya Gana Da Baki Amurkawa Bi Da Bi
Yankin na da nisan kilomita 200 tsakanin shi da babban birnin kasar, N’Djamena.
Hukumomin kasar na zargin mayakan Boko Haram daga Nijeriya ne da dasa bam din, inda suka ce wannan na nufin ‘yan ta’addar na shirin sabunta hare-harensu a iyakar Chadi.
Sojojin kasar su kan kai hari akai-akai tare da kashewa da kuma kama ‘yan ta’addar, inda su ma ake kashe su a wasu lokuta, duk da samun saukin lamura a ‘yan shekarun nan.
Tafkin Chadin ya yi iyaka da wasu kasashen Afirka irin su Nijeriya, da Nijar, da kuma Kamaru, sannan yana fama da hare-haren mayakan ‘yan ta’adda irin su Boko Haram, da ISIS da kuma ISWAP.