Shugaban kasar Najeirya Bola Tinubu, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a jiya Alhamis 9 ga wata, a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.
Yayin ganawar tasu, Wang Yi ya isar da gaisuwa da kyakkyawan fatan sabuwar shekara daga shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa shugaban Najeriya. Ya ce, mai girma shugaba Tinubu ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Sin cikin watan Satumban bara, inda shi da shugaba Xi Jinping suka sanar da raya huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni, don tabbatar da raya huldar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.
- Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Da Wasu Matasa ’Yan Wasan Peking Opera Suka Aika Masa
- Alkaluman Hauhawar Farashi Na Sin Sun Karu Da Kaso 0.2% A 2024
Ya ce huldar dake tsakanin Sin da Najeriya misali ce ta ingantacciyar huldar Sin da kasashen Afirka, kuma ta wuce hulda tsakanin kasashen biyu, kamata ya yi bangarorin biyu sun kara hadin gwiwarsu don raya kyakkyawar makomar al’ummun kasashen biyu a dukkan fannoni a sabon zamani, da samar da abin koyi ga hadin kan kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa.
Wang Yi ya jinjinawa matsayin da Najeriya ke kai, na nacewa ga manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, kuma Sin na goyon bayan Najeriya da ta bi hanyar raya kai bisa halayenta, da mara mata baya ga aikin yaki da ta’addanci, da kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali a wannan yanki, da kara mata kwarin gwiwar taka karin rawarta a duniya.
A nasa bangaren, shugaba Tinubu ya isar da sahihiyar gaisuwarsa ta bakin Wang Yi ga shugaba Xi Jinping. Ya ce, Najeriya ta dora muhimmanci matuka kan huldar kasashen biyu, kuma tabbatar da ci gaban da aka samu a taron koli na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, na da ma’ana sosai ga bunkasar kasarsa. Ya ce, Sin na da ingantaciyyar kima a duniya, kuma yana fatan Sin za ta ci gaba da goyawa Najeriya baya don ta kara taka rawa a cikin harkokin duniya.
Ban da wannan kuma, shugaba Tinubu ya bayyana juyayi ga aukuwar bala’in girgizar kasa a jihar Xizang. Yana mai jinjinawa matakin ceto kan lokaci da gwamnatin Sin ta dauka.
Har ila yau a dai jiyan, Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa na Najeriya Yusuf Tuggar da kuma ganawa da manema labarai tare. (Amina Xu)