Borussia Dortmund na sha’awar sayen dan wasan gefe na Man U Jadon Sancho, inda ake tattaunawa kan yarjejeniyar aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
United ta sayi Sancho daga Dortmund a shekara ta 2021 a kan kudi fam miliyan 73, amma kuma tun watan Agusta bai buga wa United wasa ko daya ba sakamakon rashin jituwar dake tsakaninsa da kocin kungiyar Eric Ten Hag.
Idan hakan ta tabbata Sancho zai koma kungiyar ta Borrusia Dortmund dake buga gasar Bundesliga a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.
- Man U Ta Maye Gurbin Eriksen Da Zai Yi Jinyar Watanni Uku
- Bai Kamata Chelsea Ta Zauna A Matsayi Na 10 A Gasar Firimiya Ba – Pochettino
Man Utd ta sayi Sancho daga Dortmund a bazarar 2021 a kan fam miliyan 73 inda tun bayan zuwansa ya buga masu wasanni 58 inda ya jefa kwallaye 9 a raga.
Kwantiragin dan wasan na Ingila a Old Trafford zai kare ne a shekarar 2026, inda United ke da zabin tsawaitawa tsawon shekara guda.
Tun lokacin da dan wasan mai shekaru 23 ya shiga shafukan sada zumunta inda ya karyata ikirarin da kocin kungiyar Eric Ten Hag ya yi na cewa Sancho yana atisaye shi kadai ba tare da sauran abokan wasansa ba ya sa ba a sake kiransa a cikin tawagar yan wasan kungiyar ba.
Abin lura a yanzu shi ne shin Borussia Dortmund za ta iya biyan cikakken albashin Jadon Sancho ko za su yi fatan United ta iya taimaka musu ta biya wani kaso na albashin dan wasan.
Idan zai tafi Dortmund na tsawon watanni shida, ya taka rawar gani kuma ya dawo Manchester United to tabbas darajar kasuwarsa za ta yi yawa fiye da yadda take a yanzu.
Sai dai a halin yanzu, akwai sauran aiki da yawa a kan wannan yarjejeniya, amma Borussia Dortmund tana sha’awar kuma tana tattaunawa da Manchester United kan Jadon Sancho.