Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tayi rashin nasara a hannun abokiyar karawarta Brighton And Hove Albion a wasan da suka buga ranara lahadi.
Brighton ce ta fara jefa kwallo ta hannun Danny Welbeck kafin Gross ya jefa ta biyu bayan dawowa hutun rabin lokaci.
Pedro ya jefawa Brighton kwallo ta uku kafin matashin dan kwallon Manchester United Hannibal ya farke wa Manchester United kwallo daya.
Da wannan sakamakon ne Manchester United tayi rashin nasar sau uku a wannan kaka ta bana yayinda take da maki shida a teburin gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp