• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

by Ra'ayinmu
10 hours ago
Amfani

Wata Jarida da ke wallafa rahotanninta a kafar Internet, a watan Disambar 2023, ta wallafa labaran binciken da wani ɗan jaridar na kafar a binciken ɓoye, ya yi basaja a matsayin ɗalibai mai neman gurbin ƙaro karatu a wata Jami’ar da ke a  Kwatano.

Wannan basajar ɗan jaridar ta ba shi dama bankaɗo yadda ake samu shedar karatun Digirin ɗan Kwatano a cikin mako shida kacal tare da kuma yin tafiya aikin yiwa ƙasa hidama wato NYSC.

Wannan aikata badaƙalar ɗaya ce kawai daga cikin sauran dubban baƙala da ta fito fili a ƙasar wanda hakan ke nuna yadda samun dabbban Takardun karatu na bogi a ƙasar da kuma aikata sauran mayan ayyukan badaƙala.

  • 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
  • Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

Kafin fallasa wannan baƙalar, ko a watan Nuwambar 2020, wata jaridar ƙasar ta fallasa wasu aƙaluma da suka nuna yadda aikata ɗabi’ar badaƙa ke ƙara yin ƙamari a ƙasar, inda dubun wasu ta tuno, a yayin wata tantance ma’aikata, a jihar Filato, inda aka gano, Takardunsu na karatu na bogi ne.

Ƙarin wani abin takaicin shi ne,lamarin ba wai kawai ya tsaya kan ƙananan ma’aikata bane, amma yadda ɗabi’ar, ke ci gaba da zama ruwan dare a ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Kazalika, har yanzu batun tsohon shugaban Majalisar Wakilai wato Salisu Buhari, na 1999, na yin amfani da Takardun karatu na bogi da ya yi iƙirarin ya samo daga Jama’iar Toronto, baƙalar na ci gaba da kafa babban misali, a ƙasar.

Badaƙalar ta sa, ba ta tsaya nan ba, ya kuma ƙaryar shekarun na haihauwa, domin kawai, ta tsaya takarar siyasa, a wancan lokacin, wanda kuma ya nuna turjiya daga sauka daga muƙamin na nsa duk da ɗimbin hujjojin da suka bayyana a kansa, inda bayan komai ya bayyana ƙarara, ya sauka daga kan muƙamin shugabancin Majlisar a 2000, ya kuma ɓarke da kuka a Majalisar, ya amsa cewar, Takardunsa na bogi ne.

Haka ita ma, tsohuwar ministan kuɗi Kemi Adeosun, aka samu hanunta dumu-dumu a cikin irin wannan ɗabi’ar ta aikta badaƙala, bayan an gao cewa, Takardar ta neman tsame ta daga yi wa ƙasa hidima, ta bugi ce.

Haka zalika, aikata irin wannan badaƙalar ta kwana-kwanan ita ce ta ministan ƙirere, kimiyya da fasaha wato Uche Nnaji, wanda shi ma, ya gabarwa da shugaban ƙasa Takardun karatunsa na bogi, da ya yi iƙirarin ya samo daga jami’ar Nsukka, domin a tantance shi, ya zama ministan wannan ma’aikatar.

Wannan badaƙalar, za iya cewa, kusan ta faro ne, tun a cikin Azuwan makaranta wanda hakan ya nuna cewa, ba daga kan ‘yan siya ta samu asali ba, inda masu sanya ido kan ɗaliban da ke kan zana jarrabawa, inda masu sanya idon, ke yiwa wasu ɗaliaban jigar Takardun satar amsar jarrabawa.

Hakazalika, lamarin ya kuma nuna jadda wasu iyayen ke haƙilon ganin ‘ya’yansu, sun zana jarrabar kammala sakandare a cibiyon zama jarrabawa, na neman na neman sa’a, domin kawai ‘ya’yansu, su lashe jarrabawar.

Akwai kuma batun yadda ake sauya samakaon jarrabawa yayin kwafo sakamakon WAEC ta hanyar haɗa baki, da wau gurɓatattun ma;aikata a ma’aikatun ilimi da kuma bayanan shidar karatun mutum wato CƁ da Takarun bogi na NYSC.

Irin wannan lamarin, ya kuma haifar da samun wasu matasan ƙasar na shiga cikin mummunar ɗabi’ar damfara ta kafar Internet, wato waɗanda ake yiwa laƙabi da, ‘Yan Yahoo-Yahoo”, inda suka damfarar mutane miliyoyin kuɗaɗe, ta nahyar yin kutse a cikin Asusun ajiarsu na Bankuna.

Lamarin na kuma sanya wasu ma’aikatan Gwamnati da wasu sanatoci, yin arigizo a cikin kasafin kuɗi da kuma biyan wasu ‘yan kwangila kuɗaɗen yin kwangila wanda daga baya, su yi watsi, da aikin, bayan sun karbi kuɗin yin kwagilar.

Abin dubi a nan shi ne, idan har masu aikata irin ɗabi’ar za su iya wucewa da tunanin manyan hukumomin ƙasar wajen yin amfani da Takardun karatu na bogi, kamarsu, majalisar dattawa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya DSS, hakan ya nuna ƙarara, orin gazarwar waɗannan hukumomin, musamman duba da yadda minista sukutum ya miƙa gabatar da Takardun karatu na bogi, domin a tantance shi a muƙamin minista. 

A ra’ayin wannan Jaridar, ya zama wajibi, wannan lamarin, ya sama na ƙarshe da wasu ke aikata wa a ƙasar kuma ya zama wajibi, majalsar ƙasar ta tabbatar ana gudanar da cikakken bincike a ɗaukacin mayan makarantun ƙasar da kuma samo sahihan bayanai na ministocin da ke kan muƙamasu da shuwagannin hukumomin Gwamnati da kuma na ‘yan majalisar da suka samu Takardun sheda na NYSC.

Bugu da ƙari, jami’oin ƙasar da kuma mahukaunata  a NYSC, su rinƙa yin amfani da sahihiyar kafar intanet da aka aminta da ita, wajen wallafa sunayen wa rijista.

Kazalika, ya zama wajibi, a rinƙa hukunta duk ɗan ƙasar da aka same shi, da aikata wannan mummunar ɗabi;ar domin hakan ya zama izina, ga sauran masu tunanin aikata hakan, a gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025
Manyan Labarai

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Next Post
Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

LABARAI MASU NASABA

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

October 24, 2025
Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

October 24, 2025
An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

October 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.