Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma ku ci ku sha, har farin zare ya bayyana a gare ku daga baƙin zare na alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa dare” Suratul Baƙara aya ta 187.
Wannan aya ta bayyana mana lokacin da azumi yake tuƙewa, watau dare. Dare kuma yana shiga ne daga lokacin da rana ta faɗi. Saboda haka azumi yana ƙarewa ne da shigar dare. An karɓo hadisi daga Umar ɗan Khaɗɗabi Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Idan dare ya fuskanto, yini kuma ya juya baya, rana kuma ta faɗi, to, lokacin sha ruwa ya yi” Bukhari[#1954] da Muslim [#1100].
Gaggauta Buɗa-Baki: Akwai hadisai da suka tabbatar da haka;
1. An karbo hadisi daga Sahalu dan Sa’adu, Allah Ya ƙara yarda a gare shi. Lalle Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Mutane ba za su gushe ba cikin alheri matuƙar suna gaggauta buɗa-baki” Bukhari [#1957] da Muslim [#1098]
2. An karbo hadisi daga Abu Huraira Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce:” Addini ba zai gushe ba yana yin rinjaye da galaba ba, matuƙar mutane suna gaggauta buɗa baki. Ku gaggauta buɗa-baki, domin Yahudu da Nasara suna jirkinta shi” Hadisi ne mai kyau Abu Dawud [#2353] da Ibnu Maja [#1689] da Ahmad [#9810] da Ibnu Abi Shaiba [#8944].
Imam an-Nawawi Allah ya yi masa rahama yana cewa: “A cikin wannan hadisi akwai zaburarwa a kan gaggauta buɗa-baki bayan an tabbatar da fuɗuwar rana, kuma al’amarin al’ummar Musulmi ba zai gushe ba cikin tsari da alheri matuƙar suka kasance suna tsare wannan sunna, idan kuma suka jirkinta yin buɗa-baki, to , alama ce da take nuna za su faɗa cikin wani tasku” an-Nawawi; al-Minhaju Sharhu Sahihi Muslim [7/206] . Ibnu Hajar Allah ya yi masa rahama ya ce: “Addini ya yi galaba da rinjaye yana lazimta wanzuwar alheri” Fathul Bãri [4/555].
Abul Walid al-Baji Allah ya yi masa rahama ya ce: “Mutane ba za su gushe ba game da addininsu suna cikin alheri matuƙar suna gaggauta buɗa-baki a bisa tafarki na sunna. Gaggauta buɗa-baki shi ne kada a yi jinkirin shan ruwa bayan rana ta faɗi domin nuna kai maƙura da matuƙa wajen ibada da ƙudurce cewa azumi bai yi ba idan aka sha ruwa bayan rana ta faɗi…” al-Baji; al-Muntaƙã Aharhul Muwaɗɗã [2/42].
Hukuncin Gaggauta Buɗa-baki:
Mustahabbi ne mai azumi ya gaggauta buɗa-baki bayan ya tabbar da rana ta faɗi. Duba al-Ƙadi Abdulwahab; al-Ma’unatu [1/347] da Ibnu Ƙudama; al-Muguni [3/174], da Ishaƙ bin Mansur; Masa’ilul Imami Ahmad wa Iahaƙ bin Rahuya [3/1224].
Yana daga cikin sunna gaggauta buɗa-baki. duba Ibu Abi Zaid al-Ƙairawani, ar-Risalatu [shafi na 83] da Ibni Abdilbarri; al-Kafi [1/350] da al-Ƙarafi; az-Zakhiratu [2/510] da Muhd. Binu Yusuf; at-Taju wal-Iklilu [3/304].