A watanni uku na farkon bana, yadda kasar Sin ta fitar da Deepseek, samfurin kirkirarriyar basira ta AI, da ma fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2”, ya yi matukar jawo hankalin kasashen duniya, wadanda kuma suka shaida yadda kasar Sin ke tabbatar da bunkasa mai inganci, da ma yadda kasar ke kara kwarewarta ta fannin kirkire-kirkire.
Sai dai ba Deepseek da Ne Zha 2 su kadai ba ne, kasar Sin na tabbatar da ci gaba da kirkire-kirkire a fannoni daban daban, kuma hakan ya faru ne sakamakon yadda kasar ta shafe shekaru gommai tana ta bude kofarta ga kasashen ketare.
- Mastalar Tsaro: Jihohi Sun Kashe Naira Biliyan 214 Wajen Sayen Makamai
- Koch Usman Abdullahi Zai Jagoranci Kano Pillars A Karon Farko Bayan Dakatarwa
A ganin kasar Sin, ya zama dole a bude kofa ga kasashen ketare don samun tabbatuwar ci gaban kasa. Haka kuma saboda yadda kasar Sin ke ta hadin gwiwa da kasashen duniya da kuma koyi daga wajensu, kasar ta tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta da kuma kirkire-kirkire. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta yi ta raba damammaki da ma nasarorinta da kasashen duniya. Akasin haka, wasu kasashe sun yi ta katse huldar tattalin arziki tare da kafa shingaye ga sauran kasashe, a yunkurin kiyaye fifikon da suke da shi a wasu fannoni,wadanda kuma suka yi ta kakaba wa sauran kasashe karin harajin kwastam, don neman farfado da tattalin arzikinsu.
Sai dai ko kwalliya za ta biya kudin sabulu?
Mu dauki harajin fito a matsayin misali, wanda shugaba Donald Trump na Amurka ke kallonsa a matsayin kalma mafi dadi a cikin kamus, wanda hakan ya sa sabuwar gwamnatin Amurka ta yi ta daukar kwararan matakan haraji, har ma a kwanakin baya, ta sanar da sanya haraji na ramuwar gayya a kan kasashen da ke cinikayya da ita. A ganin gwamnatin Amurka, hakan zai taimaka wajen kare masana’antu na cikin kasar tare da samar da karin guraben aikin yi. Sai dai ko za ta cimma burinta? A hakika, sanya haraji a kan kayayyakin da take shigowa da su daga sauran kasashe, zai haifar da karuwar kudaden da kamfanonin cikin gidan kasar suke kashewa, sakamakon haka, wasu kamfanoni ba yadda za su yi sai dai su sallami wasu ma’aikatansu. Ban da haka, ta la’akari da tsadar kudin da ake biyan ma’aikatan cikin kasar da ma rashin cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki a kasar, da wuya Amurka ta cimma burinta na tilasta wa kamfanonin kasashen waje su kafa masana’antu a kasar. Kwanan nan, jami’an kungiyar tarayyar Turai sun yi gargadin cewa, matakin kakaba haraji na ramuwar gayya da Amurka ta dauka ka iya haddasa raguwar ma’aunin tattalin arziki na GDP da kaso 7% a fadin duniya. Sai kuma a hasashen da cibiyar nazari ta jami’ar Yale ta kasar Amurka ta yi, idan kasashen duniya sun dauki matakan ramuwar gayya, biyowa bayan harajin da Amurka ta sanya musu, lallai ma’aunin GDP din kasar Amurka zai ragu da kaso 1%. A zahiri dai, a zamanin da muke ciki na samun dunkulewar tattalin arzikin duniya, kariyar cinikayya ba za ta haifar da da mai ido ba, maimakon hakan, hasarori ne kawai za ta haddasa ga kowa, ciki har da wanda ya dauki matakin.
Har ila yau a kan batun haraji, a karshen bara, kasar Sin ta cire harajin kwastan a kan dukkanin kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da ita, ciki har da wasu kasashe 33 dake nahiyar Afirka, matakin da a hannu guda ya saukaka hanyoyin shigowar amfanin gona na kasashen Afirka cikin kasuwar kasar Sin don biyan bukatun gidanta, a dayan hannu kuma, ya taimaka ga saukaka fatara da ma bunkasuwar sana’o’i a kasashen Afirka. Wato ke nan, Sin da kasashen Afirka sun tabbatar da cin moriyar juna da samun nasara tare ta hanyar bude kofa da ma hada gwiwa da juna.
Lallai kashe fitilun wasu ba zai taimaka ga samar da haske ga wasu ba. A zamanin dunkeluwar tattalin arzikin duniya, tuni kasa da kasa sun zamanto masu matukar alaka da juna a tattalin arzikinsu, kuma ko kadan ba zai yiwu ba su katse huldar tattalin arziki da juna.
Ba shakka, bude kofa da hadin gwiwa da juna kalmomi ne mafi dadi, wanda a baya an shaida hakan, kuma zai ci gaba da tabbata a gaba. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp