Wata budurwa mai suna Fatima Ismail ta roki wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rigasa a Jihar Kaduna, da ta umarci tsohon saurayinta, Abubakar Shu’aibu ya biya ta Naira 180,000 da ya karba aro a wajenta.
Ta shaida wa kotun cewa ta bai wa Shu’aibu rancen Naira 230,000 don gyara motarsa, kuma ya zuwa yanzu Naira 50,000 kacal ya biya ta.
- Kasashen Afirka Da Jama’arsu Sun San Mai Kaunarsu Na Hakika
- Mutane Sun Daina Fallasa Barayin Gwamnati A Nijeriya — Zainab Ahmed
Ta ce duk kokarin da ta yi don tsohon saurayin nata ya biyan kudin ya ci tura.
A nasa bangaren, Shuaibu ya ce tsohuwar budurwar tasa ba ta bayyana ko kudin da ta ba shi aro ba ne ko kyauta ta ba shi.
“Ba ta son ganina cikin damuwa.
“Duk lokacin da ta ganni a cikn wani yanayi, sai ta tambaye ni ta ba ni kudi,” in ji shi.
Ya shaida wa kotu cewa ba shi da aiki.
Ya yi alkawarin biyan N20,000 duk wata har zuwa lokacin da zai kammala biya bashin.
Alkalin kotun, Malam Abubakar Salihu -Tureta, ya yanke hukuncin cewa wanda ake kara zai rika biyan N30,000 duk wata tun daga makon farko na watan Janairun 2023.