Garba Shehu, hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa tsohon shugaban yana jinya a ƙasar Birtaniya.
Shehu ya shaida wa LEADERSHIP cewa Buhari ya tafi Birtaniya domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba duk shekara, amma ya kamu da rashin lafiya a lokacin da yake can.
- Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi
- Gwamnatin Kano Ta Haramta Shigo Ƙarafu Daga Arewa maso Gabas
Ya ce yanzu haka yana samun sauƙi ƙarƙashin kulawar likitoci.
“Gaskiya ne cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba shi da lafiya. Yana jinya a ƙasar Birtaniya,” in ji Shehu.
“Ya tafi domin duba lafiyarsa ta shekara-shekara, amma sai ya kamu da rashin lafiya a can. Abin farin ciki shi ne yana cikin samun sauƙi sosai. Muna masa fatan Allah Ya ba shi sauƙi.”
Ko da yake ba a bayyana irin rashin lafiyar da ta kama shi ba, wannan bayani ya kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo game da lafiyar Buhari, musamman bayan da mutane suka lura da jinkirin dawowarsa daga ƙasar waje.
Buhari ya bar mulki a watan Mayun 2023 bayan ya kammala wa’adinsa na biyu.
A lokacin da yake shugaban ƙasa, ya saba shafe lokaci a Birtaniya domin neman lafiya.
Shehu dai bai faɗi ranar da Buhari zai dawo gida Nijeriya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp