Mamman Daura, ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa Buhari ya kasance cikin ƙoshin kwana ɗaya kafin rasuwarsa a wani asibiti da ke Landan.
A wata hira da jaridar ThisDay, Daura ya ce ya ziyarci Buhari da yammacin ranar Asabar, 13 ga watan Yuli, a asibitin da ake kula da shi.
- Buhari Da Ya Daɗe Da Rasuwa Idan A Asibitocin Nijeriya Ake Duba Shi – Adesina
- Trump Ya Bai Wa Rasha Kwanaki 50 Ta Kawo Ƙarshen Yaƙinta Da Ukraine
Ya ce Buhari yana hira, dariya, kuma yana fatan dawowa Nijeriya a cikin makon nan.
“Mun kasance tare da shi a ranar Asabar, muna hira da dariya. Buhari yana cikin nishaɗi a asibitin da ke Landan,” in ji Daura.
Daura ya ƙara da cewa Buhari ya riga ya shirya dawowa Nijeriya.
“Ya shirya tafiya gida bayan ya samu lafiya, kuma ya tabbatar da cewa an biya kuɗin otal na duk wanda ya zo Landan saboda shi kafin tafiyarsa,” in ji shi.
Daura ya ce ya bar asibitin da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Asabar, tare da alƙawarin dawowa ranar Lahadi domin sake duba Buhari.
“Na baro shi da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Asabar. Yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana jiran ganin likitansa da safiyar ranar Lahadi.”
Sai dai kuma, abubuwa sun canza a ranar Lahadi.
“Cikin dare, ya fara fama da matsalar numfashi. Likitoci suka garzaya domin ba shi kulawa, amma da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, rai ya yi halinsa,” in ji Daura.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an ɗauko gawar Buhari daga Birtaniya zuwa Nijeriya da safiyar ranar Talata.
Ana sa ran shugaban ƙasa Bola Tinubu zai tarbi gawar a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.
Za a yi jana’izarsa a yau a garinsu na Daura, a Jihar Katsina.
Buhari ya zama shugaban ƙasa na mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan ya sake zama shugaban ƙasa a mulkin dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023.
Ya rasu yana da shekaru 83.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp