Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bai wa wasu ‘yan kasashen waje 286 takardar shaidar zama ‘yan Nijeriya, inda ya bukace su da su kasance ‘yan na gari domin cin gajiyar duk wani hakki da alfarmar da aka ba su.
“Kun yi mubaya’a ga Nijeriya. Lokacin da kuka bai wa Nijeriya soyayya da amincinku, sai ta mayar muku da soyayyar ta da amincinta a gare ku.”
- Kowa Ya Yi Da Kyau Zai Ga Da Kyau
- Ya Shiga Hannun ‘Yansanda Bayan Sayan Bindiga Don Kashe Mahaifansa
Shugaban ya shaida wa wadanda suka ci gajiyar shirin a wani taron da aka yi a fadar gwamnatin tarayya a Abuja a yau Alhamis.
Shugaba Buhari, ya bayyana cewa daga cikin ‘yan kasashen waje 286 da aka bai wa takardar shaidar zama ‘yan Nijeriya, 208 sun karbi takardar shaidar zama ‘yan kasa, yayin da 78 suka samu takardar shaidar rajista.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya bukace su da su bayar da gudumawa mai kyau kuma mai amfani ga ci gaba da jin dadin al’ummomin da suke zaune a kasar nan, inda ya kara da cewa a matsayinsu na ‘yan kasa dole ne su kasance masu bin ka’idojin kasa da kasa da ka’idar aiki.
“Ana sa ran ku kasance masu mutunta dukkan hukumomin da aka kafa.
“Duk wadanda suka shafi al’amuran shige da fice su bai wa sabbin ‘yan kasarmu shaidar doka cikin gaggawa. Haka kuma ya kamata kananan hukumominsu su taimaka wajen hada kansu a cikin al’umma domin su samu damar cin gajiyar duk wani hakki na dan Nijeriya,” in ji Buhari.
Yayin aiwatar da ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi, a babi na uku, sashe na 25-31 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya, 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), shugaban ya shaida wa sabbin ‘yan kasar cewa Nijeriya kasa ce da ta hade da ka’idojin samun dama, daidaito, da ‘yanci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
“Ko daga ina kuka fito, ko wace irin imani kuka yi, kasar nan ita ce kasarku. Tarihinmu yanzu ya zama tarihinku, al’adunmu kuma yanzu sun zama al’adunku ne. Nijeriya ita ce gidanku da abin alfahari da farin cikinku.
Ya kara da cewa, “A bisa manufofinmu na kawo sauyi na bin ka’ida da tsare-tsare na gaskiya, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai aka bai wa izinin zama ‘yan Nijeriya,” in ji shi.
Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shekarar 2020 ta dauki tsarin aiki na kasa don kawar da rashin jihadi, don haka ne ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya kaddamar da babban kwamitin gudanarwa na kawar da rashin jiha a Nijeriya nan da shekarar 2024.