Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya bukaci matasa da su nemi ilimi ba don aikin gwamnati ba, don babu “ragowar wuraren aiki a gwamnati.”
Ya kuma bukaci matasa da su rika sanin tarihi domin gujewa tafka kura-kuran da na baya suka tafka. Jaridar Punch ta rahoto.
A cewar wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya sanyawa hannu a ranar Laraba, Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Sarkin Daura, Faruk Faruk, a fadarsa.
Ya roki iyaye su koya wa yaran su dabi’u nagari, wadanda suka hada da tsoron Allah, mutunta hukuma da yin rayuwa mai ma’ana ta hanyar ci gaba da neman ilimi.
Ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata a rika koyar da yara kanana tarihi, domin zai yi wuya su kasance masu kishin kasa da rikon amana da mutuntawa, in basu san cikakken tarihin asalin Kasar su ba.