Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun ‘yan uwa da abokan arziki wajen miki ta’aziyyarsa na rashuwar tsohon Sufeton ‘Yansandan Nijeriya, Mustapha Balogun.
A sakon ta’aziyyar wanda mai ba shi shawara a bangaren watsa labarai, Mista Femi Adesina, ya sanya wa hannun ranar Juma’a aka kuma raba wa maneam labarai a Abuja, ya kuma mika ta’aziyyar ga rundunar ‘yansandan Nijeriya.
Buhari ya ce a Balogun, ya inganta aikin ‘yansanda a lokacin yana shugabantar rundunar ta yadda suka gudanar da aikinsu kamar yadda tsarin dimoikradiyya ya tanada.
Talla
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya yafe masa kurakuransa.
Talla