Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nadin sirikinsa, Ahmed Halilu a matsayin Manajan-Darakta na Kamfanin buga kudi na kasa.
Halilu, wanda wan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya rike kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa, a ranar 16 ga watan Mayu.
- Ancelotti Ya Kafa Tarihi A Real Madrid
- Sin Ta Yi Watsi Da Rahoton MDD Game Da Batun Kare Hakkin Bil Adama A Xinjiang
LEADERSHIP Hausa ta jiyo daga majiya mai tushe cewa shugaban ya amince da nadin ne bisa shawarar gwamnan babban banki na kasa (CBN), Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC.
Halilu na da kwarewa a harkar banki sama da shekaru 23, inda ya yi aiki da African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank Plc.
Ya halarci kwas na Manyan Ma’aikata karo na 39 a 2017 na cibiyar National Institute for Policy & Strategic Studies Kuru, Jos inda ya samu lambar girma ta na National Institute, mni.
Halilu, ya yi digirin farko a fannin Noma B. (Agric), Masters in Business Administration da kuma Masters in International Affairs & Diplomacy duk a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Haka zalika, mamba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Nijeriya, NIM.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp