Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya fada a wani taron manema labarai da aka saba yi a yau Alhamis cewa, a yayin bullar cutar kyandar biri, ko kuma lokacin bazuwar sabuwar cutar huhu ta COVID-19, wato yayin da ake tinkarar abubuwan gaggawa na lafiyar jama’a, tsohuwar matsalar wariyar launin fata ga ‘yan kananan kabilu a Amurka tana kara bayyana.
Don haka ya kamata Amurka ta daina kokarin zama wata malama, ta kara yin ayyuka masu inganci, don tabbatar da daidaito da kare hakkin bil’adama na ‘yan kananan kabilun kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, a baya-bayan nan ne cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka (CDC), ta sanar da cewa, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kyandar biri a Amurka ya zarce mutum 18,000, wanda hakan ya sa ta kasance kasar da aka fi tabbatar da yawan masu harbuwa da cutar a duniya.
A cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka, ‘yan asalin Latin Amurka, da kuma ‘yan Afirka wadanda ke da kusan kashi 30% na yawan al’ummar Amurka, wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kyandar biri, sun wuce kashi 60 cikin 100, bisa na dukkan masu kamuwa da cutar a Amurka, amma kashi 10 cikin 100 na allurar rigakafin cutar kyandar biri ne aka ware wa ‘yan asalin Afirka, da suka kai kimanin 33 cikin kashi 100 na jimillar wadanda aka tabbatar suka kamu da cutar a Amurka.
Binciken da aka yi a Amurka ya nuna cewa, a lokacin yaduwar annobar COVID-19, ‘yan asalin Latin Amurka, da na Afirka dake Amurka, sun fi fararen fata kamuwa da cutar da kusan ninka uku, kuma adadin wadanda suka mutu sakamakon hakan ya ninka na fararen fata har sau biyu.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)