A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministoci bakwai da majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar da su.
Rukunin farko da aka rantsar sun hada da Henry Ikechukwu Ikoh – Jihar Abia, Umana Okon Umana – Jihar Akwa Ibom, Odum Odih – Jihar Ribas, da Ademola Adewole Adegoroye – Jihar Ondo.
Kashi na biyu da aka rantsar sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub – Jihar Kano, Goodluck Nnana Opiah – Jihar Imo, da Egwumakama Joseph Nkama – Jihar Ebonyi.
A ranar Alhamis kuma, shugaba Buhari ya nada sabbin Ministoci sannan kuma ya sauya wa wasu ministocin ma’aikatu.
An mayar da karamin ministan lafiya, Dr. Adeleke Mamora zuwa ma’aikatar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire a matsayin babban minista, yayin da karamin ministan ayyuka da gidaje, Muazu Jaji Sambo, aka mayar da shi ma’aikatar sufuri.
Sabon nadadden Minista, Umanna Okon shine ministan ma’aikatar Neja Delta, yayin da karamar ministar muhalli, Sharon Ikeazor aka mayar da ita karamar minista a ma’aikatar harkokin Neja-Delta.
An mayar da Karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki zuwa karamar ministar ma’aikatar ma’adinai da karafa, yayin da Umar Ibrahim El-Yakub ya zama karamin ministan ayyuka da gidaje.
Sauran sabbin kananan ministocin: Goodluck Nanah Opiah, ma’aikatar Ilimi; Ekumankama Joseph Nkama, ma’aiktar lafiya; Ikoh Henry Ikechukwu, ma’aiktar kimiyya da fasaha; Odum Udi, ma’aiktar muhalliy da Ademola Adewole Adegoroye, ma’aiktar sufuri.