Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar a Jihar Ondo, wanda ya tabbatar da sake zaɓen Gwamna Lucky Aiyeditawa.
Ya bayyana cewa masu zaɓe sun nuna gamsuwarsu da jam’iyyar da gwamnan ta hanyar kaɗa ƙuri’a, kuma wannan ya kamata sauran masu ruwa da tsaki su mutunta.
- Tura Ta Kai Bango, Zanga-Zanga Ta Kutsa Kai Har Gidan Buhari Da Sarkin Daura
- Buhari Ya Kai Ziyarar Jaje Jihohin Borno Da Jigawa
Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce sakamakon zaɓen ya nuna ƙarfin dimokuraɗiyya a Nijeriya, ƙasa mai girma da bambancin al’adu. Ya kuma buƙaci sabon gwamnan da ya mayar da hankali kan manufofin da za su ƙarfafa tattalin arziki, da rage rashin aikin yi da hauhawar farashi, tare da aiwatar da shirye-shiryen jin daɗin al’umma.
Tsohon Shugaban ya kuma jinjinawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na rage matsalolin da aka gani a zaɓukan baya. Ya yi fatan alheri ga Gwamna Aiyeditawa da tawagarsa a wa’adin mulkinsu.