• English
  • Business News
Wednesday, August 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buhari Ya Umarci Manyan Hafshoshin Soji Da Su Koma Yankin Arewa Maso Gabas

by Abubakar Abba
3 years ago
in Labarai
0
Buhari Ya Umarci Manyan Hafshoshin Soji Da Su Koma Yankin Arewa Maso Gabas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafshoshin sojin kasar nan da su koma yankin Arewa Maso Gabas don taimaka wa nasarorin da dakarun soji suka samar na yakar ‘yan ta’adda a yankin da a sauran sassa.

Buhari ya bayar da wannan umarnin ne a NDA da ke Jihar Kaduna a taron yaye wa da kuma kaddamar da daukar sabbin dalibai na karo 69 da suka hada da na sama da na kasa.

  • Kungiyar Fulani Ta Koka Kan Kisa Mambobinta A Taraba Da Kaduna
  • Kungiyar Fulani Ta Koka Kan Kisa Mambobinta A Taraba Da Kaduna

A cikin sanarwar da mai magana da da yawun fadar shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce, “Na umarci manyan hafshoshin sojin kasar da su tare a yankin Arewa Maso Gabas domin dora wa a kan nasarorin da aka samu na yakar ta’addanci a yankin, ina kuma kira ga ‘yan Nijeriya su ci gaba da ba bai wa jami’an tsaro na soji da sauran jami’an tsaro goyon baya domin a samu nasarar kawar da ta’addanci a daukacin fadin kasar nan.”

“Yin hakan na da muhimmanci matuka, musamman ganin cewa zaben 2023 na kara karatowa, na kuma daukar wa kaina alkawarin tabbatar da an gudanar da zabubbuka cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin kuma ingantaccen zabe, wannan duk nauyi ne da ya rataya a wuyan kowanne dan Nijeriya.”

Shugaba Buhari ya kuma zayyano wasu daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a shekaru bakwai, inda ya danganta ayyukan a matsayin wadanda suka fi na wanda mulkin sojin kasar nan na shekaru 38 da suka wuce.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7

Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati

Ya kuma taya daliban da aka yaye murna, inda ya ce, a yanzu ne suka bude sabon faifai a gidan soji.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Arewa Maso GabasBuhariKadunaNDATa'addancuYaye Dalibai
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 9 Da Aka Yi Safararsu A Katsina

Next Post

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Samar wa Kasar Sudan Ta Kudu Gudummawa Don Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kyautata Yanayin Jin Kai

Related

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7

3 minutes ago
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati

1 hour ago
NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano
Labarai

NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano

3 hours ago
Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago
Manyan Labarai

Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba

6 hours ago
ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
Labarai

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

7 hours ago
An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe
Labarai

An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

8 hours ago
Next Post
Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Samar wa Kasar Sudan Ta Kudu Gudummawa Don Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kyautata Yanayin Jin Kai

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Samar wa Kasar Sudan Ta Kudu Gudummawa Don Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kyautata Yanayin Jin Kai

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7

August 13, 2025
Aikin Hakar Kwal Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani Ya Fara Wuce 50% a Kasar Sin

Aikin Hakar Kwal Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani Ya Fara Wuce 50% a Kasar Sin

August 13, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati

August 13, 2025
PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

August 13, 2025
NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano

NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano

August 13, 2025
Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago

Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba

August 13, 2025
ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

August 13, 2025
An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

August 13, 2025
PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi

Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello

August 13, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita

August 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.