Buhari ya bayyana harin da aka kai kan ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah a Jihar Anambra a matsayin abun takaici da kuma abun Allah wadai.
“Mun damu matuka da ayyukan kungiyoyin da ke dauke da makamai a yankin da ma sauran sassan kasar nan. Muna sa ido sosai kan lamarin kuma muna jiran karin bayani kan martanin da jami’an ‘yansanda da sojoji da sauran jami’an tsaro suka dauka.
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Uwa Da Danta A Kwara
- Yadda Taron Marubuta Na Arewacin Nijeriya Ya Gudana A Jihar Katsina
“Al’ummar kasar nan ta yi rashin jaruman ‘yansanda hudu da sauran mataimakan Sanatan.
“A madadin gwamnati da jama’a, ina mika godiya ga wadannan jami’an tsaro da mataimakan da aka yi wa kisan gilla. Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da iyalansu a wannan mawuyacin lokaci,” in ji Buhari.
Shugaban kasar a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a ranar Laraba, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu a harin da aka kai musu.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya dawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Anambra da sauran yankunan Nijeriya baki daya.