Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana kaduwarsa bisa rahoton sace sabbin jarirai biyar da aka haifa a Jihar Anambra, ya kuma bada umarnin a magance yawaitar laifuka a yankunan ba tare da bata lokaci ba.
An yi garkuwa da jariran ne a asibitin Stanley da ke Nkpologwu a jihar.
- NIS Ta Ƙara Ƙaimin Aiki, Inda Shugabanta Ya Buɗe Sabon Ofishin Ingancin Aiki
- 2023: PDP Ta Koka Bisa Matsin Lamba Da Ake Wa Mambobinta A Zamfara
Maharan dai sun dauke jariran ne sannan suka kara gaba.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman na shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a.
Buhari ya bayar da umarnin a tsaurara matakan tsaro a asibitoci don hana sake afkuwar lamarin, inda ya ce dole ne a gaggauta shawo kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp