Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Mista Isah Jere Idris ritaya.
Wannan ya biyo bayan cikar wa’adinsa na aiki.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sabon Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 107 Da Suka Makale A Libya
Wannan ci gaba na kunshe ne cikin sanarwar karin wa’adin shekara daya da aka aike wa Jere wanda LEADERSHIP ta samu.
Takardar, mai kwanan ranar 17 ga Afrilu, 2023 mai lambar lambar CDCFIB/APPT.CG&DCG/61/VOL.IV/74Â wanda sakataren hukumar, Obasi Edozie Edmond, ya sanya wa hannu bisa umarnin ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.
An umarci Jere da ya miki ragamar aikinsa ga jami’i mafi girman mukami a hukumar.
Idan za a tuna an nada Mista Isah Jere Idris a matsayin mukaddashin ne kafin ya yi ritaya a watan Afrilun 2022 amma ya samu karin wa’adin shekara daya kafin cikar wa’adinsa.
Tsawaita wa’adin zai kare a ranar 24 ga Afrilu, 2023.