Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a Jihar Kebbi, ta bayar da takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar, Nasir Idris da mataimakinsa Umar Abubakar da ‘yan majalisar dokokin jihar 10.
Farfesa Muhammad Sani Kalla, Kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, ya kuma bayar da takardar shaidar cin zabe ga wasu zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar a zaben da aka kammala.
Jihar na da mazabu 24 na jihar sannan kuma INEC a ranar 30 ga watan Maris ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga mutane 14 da suka yi nasara a zaben majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Dokta Nasir Idris jim kadan bayan karbar satifiket dinsa, ya yabawa hukumar, da hukumomin tsaro bisa yadda jama’a suka gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba a cikin fadin jihar baki daya.
Ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka zabe su bisa yadda suka tabbatar da an gudanar da aikin cikin nasara tare da wata matsala ba, ya roki Allah da ya ba su ikon yiwa al’amuransu adalci a yayin tafiyar da mulki a jihar.
Haka Kuma ya ce ” jihar Kebbi tana da albarkatun kasa, kuma za mu yi duk abin da ya kamata na dan Adam wajen amfani da wadannan albarkatun domin ci gaban al’ummar jihar.
“Za mu ci gaba da gudanar da ayyukan da gwamnati mai ci ke gudanarwa kafin mu tsunduma cikin sababbi. Za mu samar da guraben ayyukan yi da yawa ga jama’a, musamman a fannin noma.
“ A bangaren tsaro za mu yi duk mai yiwuwa wajen maido da tsaro a yankunan da rikicin ya shafa a Kudancin jihar, domin al’ummar yankin su je gonakinsu daban-daban da kuma samar da abinci mai yawa da kuma bunkasa samar da abinci a jihar da kasa baki daya.
“Za mu cika dukkan alkawuran da muka yi wa jama’a a lokacin yakin neman zabe a jihar idan Allah ya kaimu.
Daga karshe ya bukace su da su yi addu’ar samun nasarar ga gwamnatin sa.