Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya ce kafin Wa’adin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kare a shekara mai zuwa, martabar Nijeriya za ta dawo yadda take a baya, za a shawo kan kalubalen tsaron da ya dabaibaye Kasar.
Ya kara da cewa, shugaba Buhari yana aiki ba dare ba rana domin ganin an samar da dukkan hanyoyin da za a bi wajen mika mulki cikin lumana a shekara mai zuwa, da kuma tabbatar da ganin an kawo karshen kalubalen da ake fama da shi na rashin tsaro a kasar nan.
Malami ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar bikin Sallar Idi na bana a Birnin Kebbi.
“Ina so in tabbatar muku cewa, gwamnati za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron kasar nan.
” Ina addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu domin a samun dawwamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya, tare da mika mulki cikin kwanciyar hankali a farkon shekara mai zuwa,” inji shi.