Jami’ar Bayero ta Kano ta yi bikin dawowar tsohon babban sakataren hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed zuwa jami’ar bayan ya shafe shekaru bakwai a hukumar.
Jami’ar ta shirya gagarumar liyafar murna da dawowarsa gida a ranar Asabar, 8 ga Yuli, 2023.
- Babban Sakataren Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Kasa (NUC), Farfesa Rasheed, Ya Yi Murabus
- NUC Ta Daga Darajar Kwalejin Sa’adatu Rimi Zuwa Jami’a A Kano
Babban taro ya kunshi tsofaffin mataimakan shugabanni Jami’ar da manyan jami’an gwamnati da shugabannin tsangayoyi, Daraktoci da shugabannin Sashe-sashe da sauran ‘yan Jami’ar a babban dakin taro na BUK.
Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ya ce hakika jami’ar ta yi matukar farin ciki da maraba da tsohon sakataren hukumar NUC wanda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci da ya gina BUK ta zama ta zamani.
Ya ce Jami’ar Bayero za ta ci gajiya sosai daga dimbin gogewar Farfesa Rasheed musamman a yanzu da Jami’ar ta mayar da hankalinta wajen ganin ta samu nagarta.
A nasa jawabin, Farfesa Abubakar Rasheed, ya ce kyawawan abubuwan da jami’an gudanarwar Jami’ar suka yi masa ya motsa shi, ya kuma kayatar da shi. Ya bayyana cewa har yanzu yana da ragowar shekara 3 da wata daya ya kammala aikinsa a NUC amma ya yanke shawarar janyewa ya koma aji.
Farfesa Rasheed ya ce, “Na yi kewar aji sosai kuma yanzu da na dawo, zan ci gaba da gudanar da ayyukana a Jami’ar.”
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban taron kuma tsohon mataimakin shugaban jami’ar BUK, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya ce jami’ar ta yi matukar farin ciki da karbar Farfesa Rasheed a hukumance bayan ya shafe shekaru 7 a NUC.
Ya ce Farfesa Rasheed a lokacin da yake rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jami’ar ya aiki da nuna gogewa a kusan dukkanin bangarorin Jami’ar kuma ya yi tasiri ga tsarin tafiyar da Jami’o’in Nijeriya a lokacin da yake NUC.
Babban limamin Kano kuma tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen, mataimakin shugaban jami’ar Al-Istiqama, Farfesa Salisu Shehu, tsohon shugaban ASUU na kasa, Dr Nasiru Isa Fagge, tsohon magatakarda, Dr. Sani ne ya gabatar da sakon fatan alheri. Amin Ibrahim, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Abdullahi Bichi da Farfesa S.B Ahmad na cikin mahalarta taron liyafar.