• English
  • Business News
Friday, July 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

by Leadership Hausa and Sulaiman
3 weeks ago
in Ra'ayinmu
0
Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Biyo bayan watsi da tsatsauran kudurin tilastawa ‘yan Nijeriya da suka munzalin kada kuri’a fita yin zabe a kasar nan, hakan ya sanya zuciyar akasarin ‘yan kasar da kuma sauran kungiyoyin da ke fafutukar kare ‘yancin ‘yan Adam, samun sa’ida.

Idan za a iya tunawa, shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da takwaransa da ke wakiltar mazabar Bass da Jos ta Arewa a Majalisar Daniel Asama Ago, dan jamiyyar Labour Party ne, tun da farko, suka gabatar da wannan kudurin, bisa nufin a yiwa dokar zabe ta 2022 da aka sabunta, kwaskwarima, domin ta bayar da damar tilasatwa wadanda suka kai munzalin kada kuri’ar, su yi zaben.

  • Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka
  • Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai

Kazalika, an kuma tanai huikuncin cin tarar Naira dubu 100,000, ko kuma zama a magarma na wata shida kuma dukkan hukuncin biyu, ga duk wanda ya kai munzalin jefa kuri’ar amma yaki yin zaben.

Masu goyon bayan wannan kudurin dai, sun dage kai da fata cewa, inda wannan kudurin ya zama doka, hakan zai tilatsawa wadanda suka kai munzalin kada kuri’ar fitowa kwansu da kwarkawarsu, domin sauke nauyin nasu, duba da da ‘yan kalilan ‘yan kasar da suka kai munzalin kada kuri’a ne kawai, suka fitowa yin zaben.

Shugaban Majalisar wanda ya bayyana mahimmancin wannan dakataccen kudurin, ya ce, idan kudurin ya zama doka, zai sanya a samu wanda suka kai munzalin yin zabe da dama, fitowa domin su zabi shugabannin da za su jagoranci kasar.

Labarai Masu Nasaba

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

Sai dai, ya sanar da cewa, ya janye kurin ne, bayan ya tuntubi daidaikun mutane da sauran kungiyoyi a daukacin fadin kasar.

Halin girma da dakkun da Shugaba Abba ya nuna na janye wannan kurin bayan korafe-korafen alummar asar kasar, babu shakka janyewar abu ne, da ya dace, musamman duba da cewa, tursawa ‘yan kasa a tsarin Dimokiradiyya abu ne da bai dace ba, domin kuwa a tsarin dimokiradyya ana bai wa ‘yan zabin abinda zuke bukata, wanda hakan ya sabawa batun tilasta masu yin zabe.

Bugu da kari, batun fitar jama’a yin zabe, abu ne da ake bukatar a rinka wayar da kan ‘yan kasa da nuna masu amincewa, amma bai wai ace za a tilasata su, yin zaben ba da kuma cewar, za a hukunta su ba.

Sashe na 77 (2) a cikin baka da kuma sashe na 132 (5) a cikin baka, na kundin tsarin mulkin kasar nan na1999 da aka sabunta, sun bai wa ‘yan Nijeriya da suka kai shekaru 18 kuma suke zaune a kasar kada ‘yancin yin zabe.

Sai dai, rukunin ‘yan kasar da kundin bai bai wa wannan ‘yancin ba sune, wadanda ba su yi rijista sunayen su a hukumar INEC ba da wadanda aka yankewa hukuncin kisa sai kuma masu tabin hankail.

Wani abin takaici a kasar shi ne, yadda a ranar zabuka a kasar wadda kuma aka haramta zirga-zirgar mutane da gudanar da hada-hadar kasuwanci, amma wasu ‘yan kasar sukan yi burus da wannan haramcin, su fita a ranar zabukan don gudnar da hidindumin su, inda kawai ake ganin wasu, ‘yan kalilan ‘yan kasar ne, ke fita yin zaben.

Abin har ya zama jiki a Nijeriya, domin kusan sama da shekaru uku da suka gabata, duk lokacin da za a gudanar da zabukan gama gari, ana fuskantar karancin masu fitowa kada kuri’a, wanda haka ke nuna cewa, ana samun babban kalubale.

Misali, a 2015, duba da yawan adadin ‘yan kasar da suka canci kada kuri’a su miliyan 67.42, miliyan 29.43 ne kacal, suka fito jefa kuri’a wanda wannan adadin ya nuna cewa, kaso 65 ne kacal, suka kada kuri’unsu.

Bugu da kari, a 2019, wadanda suka canci kada kuri’a su miliyan 84 ne kacal, ba su fito kada kuri’a ba, inda miliyan 28.61 ne kacal, suka fito jefa kuri’arsu, wanda hakan ya nuna sun kai kaso 34.75.

Duba da yadda ‘yan kasar suka nuna matukar bukatar son fita zaben 2023, amma wadanda suka fita zaben, amma miliyan 24.97 ne kawai suka fita zaben wanda hakan ya nuna cewa, kaso 26.72 ne kawai, suka fita zaben, daga cikin wadanda suka canci yin zaben su miliyan of 93.47.

A batu na gaskiya, adadin masu fita zabe a Nijeriya ya yi kasa matuka, idan aka kwatanta da yadda wadanda suka canci kada kuri’a a kasashen Afirka ke yin Farar dango don fita zaben.

Alal misali, alkaluman zabukan da aka gudanar a kasashe kamar irinsu Rwanda, ta kasance tana da kaso 98.2, Gabon na da kaso 59, Liberiya na da kaso 70.

Kazalika, Sierra Leone na da kaso 75 Jamhuriyar Kongo na da kaso 42, Zimbabwe na da kaso 68.86, Afirka ta Kudu na da kaso 65, Masar na da kaso 66.88, sai kuma and Ghana wadda take da kaso 60.

Irin wadannan alkaluman a Nijeriya, batun yasha ban ban, domin a zaben 2023, an samu kaso 26.74 ne.

Zaben shugaban na 2023, tamkar anyi shi ne, na kusan gumurzu wanda shuaban kasar mai ci Bola Tinubu, ya lashe zaben, ta hanyar samun kuri’u 8,794,726 kacal, duk da cewa, Nijeriya na da wadanda suka kai munzalin kada kuri’a, su sama da miliyan 100.

Mai yawa, saboda irin wannan abin damuwar na rashin fita zaben ne, hakan ya sanya Abbas Tajudden da takwaransa Daniel Asama Ago, suka gabatar da dakataccen kudurin na tilasta ‘yan kasar da suka kai munzalin jefa kuri’a fita, domin sauke ‘yancinsu, da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su.

Kin fita yin zaben da wasu ‘yan kasar da suke kai munzalin kada kuri’a, abu ne da bai dace ba.

A bisa matakin farko, abinda yafi dacewa a gano shi ne, shin me ke hada ‘yan kasar suka canci kada kuri’a ba su fita yin zaben, sannan kuma a lalubo da mafitar magance hakan.

Sai dai, wani hanzari ba gudu ba, za a iya cewa, ba su fita zuwa sauke nauyin na su ne, gazawar yadda ake tsara komai na gudanar da zabukan.

Karin wani abin takaicin shi ne, yadda wasu ‘yan zamalar ‘yan takara ‘yan siyasa ke hada baki da jami’an zabe, jami’an tsaro, inda kuma daga baya-bayan nan, suke hada baki da wasu Alakalai domin a tabka choge, a murda zabukan.

Irin wannan karfa-karfar da kuma murde zabuka ne, ke janyo karya masu Guiwar masu jefa kuri’ar, domin a bai wandanda ba su ci zaben nasara ba, wanda a lokuta da dama, wasu zabukan, ba a kammala kidaya kuri’un da aka kada.

Bugu da kari, a gefe daya kuma akwai matsalar ‘yan bangar siyasa da ke tayar da yamusti a Rumfunan zabe musamman domin su kare rayukansu daga aukwar ‘yan bangar siyasa da matsalar sayen kuri’u da kuma wallafa labarukan karya na sakamakon zabukan.

Hakazalika, wani batun mai ban haushi shi ne, na rashin hukuntan wadanda suka karyar dokokin zaben.

Karin wani abin takaicin shi ne, na yadda jam’iyyun kasar ba su da dabi’ar ilimantar da masu jefa kuri’a kuma ba su wani takamai-man shirye-shirye da suka tanada, domin yin hakan, sai dai kawai, su buge da yin farfagandar siyasa, wanda idan sun dare madafun iko, su yi watsi da magoya bayansu.

Akwai kuma batun kalubalen rashin samun samun yin rijitsa domin samun katin yin zabe wato PBC.

A bisa ra’ayin wannan Jaridar, mai makon batun matsawa wadanda suka munzalin jefa kuri’a don su yi zaben ba, kamata ya yi ‘yan Majalisar su gabatar da kudurin da zai sanya a sanya wa ‘yan kasar da suka cancanci kada kuri’a sha’awar fita sauke nauyin na su.

Yin haka ne, kadai, zai tabbatar da matsayin Hukumar Zabe ta kasa INEC, tabbacin cewa, Hukuma ce, mai cin gashin kanta.

Kazalika, ya zama wajbi INEC ta kara inganta tsare-tsaren ta kuma dole ne, duk wani jami’ain tsaro da ‘yan siyasar da aka samu da taka dokokin zabe, an hukunta su.

Wannan Jaridar na da yakinin cewa, ‘yan Nijeriya na son fita yin zabe, amma yadda ba a gudanar da zabukan a bisa gaskiya ne ke kara janyo wadanda suka canci kada kuri’ar, ba su fita, domin sauke nauyinsu.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

Next Post

Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya

Related

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
Ra'ayinmu

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

2 weeks ago
Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara
Ra'ayinmu

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

4 weeks ago
Daurarru
Ra'ayinmu

Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan

2 months ago
NCC
Ra'ayinmu

Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data

4 months ago
Ra'ayinmu

Gangamin Yaki Da Cutar Kuturta A Nijeriya

5 months ago
Karuwar Cin Zarafi Da Makomar Yara A Nijeriya
Ra'ayinmu

Karuwar Cin Zarafi Da Makomar Yara A Nijeriya

6 months ago
Next Post
Kuri

Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya

LABARAI MASU NASABA

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

July 4, 2025
‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

July 4, 2025
Yawan Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Da Ganga 177,000 A Janairu

Kungiyar MEMAN Ta Yi Maraba Da Shirin Dangote Na Rabar Da Man Fetur

July 4, 2025
NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku

NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku

July 4, 2025
Sin Na Kara Rungumar Nau’o’in Makamashi Marasa Gurbata Muhalli

Sin Na Kara Rungumar Nau’o’in Makamashi Marasa Gurbata Muhalli

July 3, 2025
Bayan Taron Haɗaka, Hankali Wike Ya Tashi — ADC

Bayan Taron Haɗaka, Hankali Wike Ya Tashi — ADC

July 3, 2025
Mai Tsaron Ragar Nijeriya, Peter Rufai Ya Rasu

Mai Tsaron Ragar Nijeriya, Peter Rufai Ya Rasu

July 3, 2025
Sin Na Fatan Yin Tafiya Bai Daya Tare Da Amurka 

Sin Na Fatan Yin Tafiya Bai Daya Tare Da Amurka 

July 3, 2025
Ƴan PDP Na Fice Wa Na Barin Jam’iyyar Ga Wike Da Ƴan Koransa –  Dele Momodu

Ƴan PDP Na Fice Wa Na Barin Jam’iyyar Ga Wike Da Ƴan Koransa –  Dele Momodu

July 3, 2025
Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 13

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 13

July 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.