A kwanan baya ne, Hukumar Sadarwa ta Kasa NCC ta sahalewa Kamfanonin Sadarwa na Kasar nan yin karin kaso 50 na kudin Data da kuma na kiran wayar tafi da gidan, inda lamarin ya haifar da cecekuce a tsakain ‘yan Nijeriya, musamman talakawa da ke amfani da kafar sadarwa.
Wannan karin ya zo ne, daidai lokacin da akasarin talakawan kasar, ke ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki, biyo bayan tsauraran tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya mai ci ta kirkiro da su.
- Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
- Sin Ta Mika Tallafin Wasu Jirage Marasa Matuka Na Inganta Noma Ga Kasar Zambia
Sai dai, batun ba boyayye ba ne, duba da yadda shekara da shekaru, masana’antun sadarwa a kasar, ba su iya gudanar da ayyukansu, yadda ya dace.
Duk da wannan karin na farashin Data da na kiran wayar da Kamfanonin suka yi, har yanzu ba su iya gamsar da ‘yan kasar da ayyukansu, wanda hakan ke kara sanyawa ‘yan Nigeriya ke fitar da rai daga ayyukan masana’antun.
A yayin da masu kamfanonin sadawar suka hakikance cewa, dole ne ya sanya suka yi karin, musamman domin su inganta gudanar da ayyukansu da samar da kayan aiki, amma ‘yan Nijeriya da dama suna kwan-kwanton kan yadda masu kamfanonin za su yi amfani da karin kudin shigarsu, domin ainganta ayyukansu.
Sai dai, idan za a yiwa wadannan Kamfanonin adalci, sun jima suna yin cajin farashinsu da sauki, musamman idan aka kwatanta da sauran fannonin.
Bugu da kari, matsin tattalin azrkin kasa, hauhawan farashin kaya, cire tallafin man fetur, karin farashin makamashi, karin farashin kudin wutar lantarki,sun kara zamowa Kamfanonin sadarwar matsala wajen ci gaba da samun riba.
Kazalika, wadannan matsalolin sun kai ga har sun shafi ma’aikatan da ke aiki a wadannan Kamfanonin, duba da yadda Kamfanonin suka gaza karawa ma’aikatansu albashi.
Sai dai, Kamfanonin sadawarwa MTN, Glo, Airtelda kuma 9mobile, suna hakilon lalubo da mafita kan yanewar kiran waya da rashin gudun da Data da rashin samun sadarwa.
Masu Kamfanonin sun bayyana cewa, ‘yan Nijeriya za su ci gaba da fuskantar ingancin ayyukan Kamfanonin, matukar za a ci gaba da fuskantar matsalar wutar lantarki da lalata masu kayan aikinsu.
Kungiyr da ke bai wa Kafanonin Sadawar Lasisi ta Kasa ALTON, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo dauki, domin a magance rashin ingancin ayyukan Kamfanonin a kasar.
Hukumar ta NCC ta alakanta rashin ignacin ayyukan Kamfanonin kan yadda ake lalata masu na’urorinsu a fadin kasar, musamman duba da cewa, gudanar da ingantaccen aikin Kamfanonin shi ne, ginshikin samar da sadarwa.
Kamfanonin sadawar a kasar nan na bukatar ayi masu garanbawul, kuma ya zama wajibi Hukumar NCC ta zargi Kamfanonin sadarwar, kan gazawar su ta rashin samar da ingantaccen aiki, musamman domin masu amfani da kakafen sadarwar, sun san da cewa, suna morar kudadensu.
Bugu da kari, ya zama wajibi Hukumar NCC ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa, ana bai wa masu amfani da kamfaninin sadarwar kariyar da ta kamata da kuma tabbatar da cewa, suna amfana da ayyukan Kamfanonin ba tare da fuskantar wata tangarda daga ayyukansu ba.
Kazaliaka, ya kamata Hukumar ta NCC ta kara mayar da hankaili wajen sanya gasa a masana’antar Sadarwar da kuma sanar da wata sabuwar kasuwa, wanda hakan zai sanya masu amfanin da Kamfanonin sadarwa a kasar za su zabi Kamfanonin sadarwar da suke ganin, za su biya masu bukatarasu, ba tare da fuskantar wata matsala.
Lokaci ya yi da Kamfanonin sadawar da ke a kasar nan, su tabbatar da cewa, suna mayarda hankali wajen bai wa masu amfani da layukan sadarwa a kasar kariyar da ta kamata, Kamfanonin su kuma tabatar da cewa, suna zuba hannun jari wajen kara inganta ayyukansu, musamman domin amfanin daukacin ‘yan Nijeriya.
Bugu da kari, yana da kyau, Kamfanonin sadarwar da ke a kasar nan, su tashi tsaye wajen lalubo da mafita kan kalubalen da masa’antar ke fuskanta, musamman domin masana;antar, ta ci gaba da dorewa.
Idan har a kasar nan, ba a dauku matakan inganta masana’antar ba, to tabbas wata rana, za ta zama sai dai Buzunta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp