• English
  • Business News
Saturday, July 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

by Rabi'at Sidi Bala
5 hours ago
in Taskira
0
Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi zamantakewr aure, musamman bangaren maza, duba da irin korafe-korafen da wasu matan ke yi akan yadda mazajensu suke boye musu samunsu, alhalin su matan ba su damu da abun hannun mazajen ba, face ma su kasance cikin tausayi tare da fafutukar neman yadda za a yi.

  • Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin
  • Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar

Da yawan wasu mazan na boye samunsu ga matayensu, ta yadda suke yi musu karyar ba su da shi, kuma ba sa wadata iyalan nasu, ya yin da gefe guda kuma suke cin karensu babu babbaka suke bushasha da kudadensu ga ‘yan’uwansu ko wasu daban, su ci me kyau, su sha me kyau, iyalansu kuma su zauna cikin tagumi.

Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; ‘Ko me ya sa mazan suke yin hakan/Me yake janyo hakan?, ko akwai wani kalubale da za a iya fuskanta game da hakan?, wacce shawara za a bawa maza masu aikata hakan, har ma da su kansu matan?’.

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Labarai Masu Nasaba

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:

Gani suke ai in su nuna suna samu kamar matan nasu za su dora musu hidima da yawa, sun gwamma ce su bar matansu da wahala. Wani ma dan rashin imani kokari yake ita matar ta ciyar da shi alhalin yana da damar sa, shi ya sa ko yaran wani lokaci in suka taso komai na mahaifiyarsu sai daga baya ya zo ana da-na-sani mara amfani a lokaci da ba shi da amfani. Rashi tausayi ne kawai kuma kusan yanzu ma kaso casain na maza haka suke, ka so daya ne suke kyautatawa iyalansu. Kalubale babba ma kuwa shi ya sa sam! yanzu auren ma ba ya karko, karshe a jefa mace hanyar da bata dace ba. Su ji tsoron Allah su daina ba dan halin mu ba, dan Allah su mata su ji tsoron Allah, dan Allah su daina rashin tsoron Allah ne yake kawo haka gaskiya, Allah kyauta.

Sunana Aisha Lawan Ya’u, daga Jihar Kano Ado Bayero Layout:

Dalilan da ya sa maza suke boyewa matansu samunsu: gaskiya san zuciya ne da rashin sanin yakamata, duk namiji me nazari zai so wadatuwar iyalansa. Kalubalen zai kasance matanka da yaranka za su samu kansu cikin kunci da rashin sanin madafa, domin kuwa duk samun mace za ta so tallafin mijinta a gareta. Shawara ga maza wannan hanya ba za ta kai ku ko’ina ba sai tashar da-na-sani, domin inda tunani wadatuwar iyalanku shi ne karin budinku. Ke kuma mace sai ki dage ku nemi sana’a, domin tallafar kanki da yaranki.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:

Batun da ake tattaunawa a wannan mako yana da matukar muhimmanci, musamman domin samun zaman lafiyar iyali. Babu shakka ana samun mazajen da ba sa yarda matan su na aure su san sirrin samun su, saboda fargabar da mazan ke da shi kan cewa, idan matan suka san suna da kudi to, sai sun yi duk yadda za su yi su raba su da wannan kudin, ta hanyar kawo korafe-korafe da matsaloli iri-iri, ta yadda duk abin da suke da shi zai kare. Don haka ake samun wasu da za su boye samunsu ga matan su, sai dai kullum su rika kukan babu. To, a gaskiya wannan ba hali ne mai kyau ba, domin kuwa masu irin wannan hali suna barin iyalinsu cikin kunci, na rashin wadatar kudin cefane, da sauran bukatun gida. Babban abin takaicin ma shi ne idan mutum yana da wadatar amma sai ya gwammaci ya bar iyalinsa cikin kunci, shi kuma ya je waje yana cin mai dadi. Lallai ya kamata mu sake tunani, mu sani fa irin wannan hali ne yake lalata tarbiyyar iyali, har ka ga yara sun fara dauke-dauke, ko bin maza. Allah ya tsare iyalinmu bakidaya daga fadawa cikin wannan jarabawa. Mu kuma Ubangiji Ya wadata mu ta yadda za mu wadata iyalinmu. Mazaje masu iyali mu ji tsoron Allah, mu sani fa cewa, iyalinmu amana ce a garemu, kuma Ubangiji zai yi mana hisabi kan yadda muka kula da su.

Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija:

Abin da na fi tunanu suna yin haka ne gudun ka da mace ta yi ta kawo musu bukatunta ne wanda kuma hakkinta ne a wajensu su yi mata su yi wa ‘ya’yansu saboda zamansu take yi, su suka kawo ta suka ajjiye ta. Shawarata bai wuce kana nema dan ‘ya’yanka da matanka da kuma ‘yan’uwanka, ka duba adalci yadda za ka kyautatawa iyayenka da ‘yan’uwanka, ka kyautatawa iyalanka da matanka. Allah ya sa mu dace

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Abu na farko shi ne; rashin adalci, kiyayya, rashin gaskiya, cin amana, wulakanci, fariya. Abu na gaba kuma na kalubalen da za a fuskanta shi ne; yawaitar munanan dabi’u, gurbacewar tarbiyya. Shawara ita ce; Jin tsoron Allah, mata kuma su kama sana’a.

Sunana Princess Fatima Zahra Mazadu:

Gaskiya ya danganta da irin mijin da mace ke tare da shi da yadda asalin suka gina soyayyarsu, shin kan gaskiya da amana ne ko ko kun ginata akan kowa da ra’ayinsa. Mafi akasarin maza tabbas suna boyewa ne saboda rikicin mata, dan wata macen tana ganin kudi a wurin mijinta hankali ya tashi sai an kashesu kafin ta samu sukuni, wani kuma ra’ayin sane kawai da rowa da bakin hali wanda shi kanshi kadai ya sani. Tsantsan rowa ne da kuma rashin yarda, meye rashin yarda? shi ne; ka boye dukiyar ka ga wanda yake mallakinka wanda ba daidai bane, da ita macen za ta yi masa hakan wallahi da duk gari sai an sani cewa ba ta son shi bata yarda da shi ba, da dai sauransu. Rashin daidaito da kuma yarda da juna zai yi karancin. San-samu su zamo daya duk abun da ka samu nata ne, duk abun da ta samu naka ne, wannan shi zai klkara zaman lafiya da kaunar juna da tausayin juna tare da jin kai, kuma kodayaushe daya zai zamo yana yabon dan’uwanshi ta fannin addu’a da kyautatawa.

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga Jihar Jigawa:

A gaskiya abun da ya sa maza suke boye samun su ga matan yanzu akwai dalilai da yawa. Kadan daga ciki shi ne; da zarar mace ta san samunka sai su dinga dorawa miji dawainiyar da ba tada wani muhimmanci to, shi ne ya sa maza suke boye samun su. Klubalen da za a fuskanta shi ne da zarar mace ta san samunka ba a fiya zaman lafiya ba, saboda kullum ta rika kawo maka bukatu barkatai da zarar bata samu ba tofa sai ai surutu. Shawarar a nan ita ce miji ya rika sauke duk wani nauyin da Allah ya dora masa, sannan ita kuma matar ta rika saka masa albarka a abun da ya zo da shi, ba tare da tana bibiyar aljihunsa ba.

Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:

So da dama tausayawan da mazajen ke samu wajen matansu kan sa su boye samun su, yanzu mata sun mike da neman kudi kuma abubuwa da dama ba sa jira daga wajen miji saboda tausayawa irin na mace, da wannan damar namiji ke amfani sai ya mike kafa ko ya samu ba zai bayyana ba, saboda yana ganin hana shi za ta yi, idan mace ta fahimci hakan dole zuciyar ta za ta bushe, tausayin mijin zai iya fita daga zuciyarta domin zuciya tana son me kyautata mata ne. Sharawata ga mazaje su daina boye samun su, su san cewa su Allah ya daurawa alhakin ciyar da iyalinsu ba matayen su ba, saboda gujewa irin haka mace tun farko kar ta ma fara daukewa mijinta ciyarwa, har gara sutura da wasu bukatunta, wani abu bayan wannan sai dai ki ba shi, bashi in ya kasa biyan wani sai ki yafe mishi.

Sunana Suwaiba Habeeb daga Gombe:

Su mazan gani suke kamar a kullum idan suna bayyanawa matansu samun su to, za su talautar da su kuma matan sun san suna samu to za su rika tambayar su bukatu daban-daban, wanda hakan kuma hakki ne a kanshi kuma ya kamata ya sauke shi. Shawarata a nan ita ce su mazan su rika yi wa matansu kyakkayawan zato, kuma su rika kokarin sauke hakkin da Allah (SWT) ya daura masu tare da kuma farantawa iyalansu daidai karfinsa.

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Wasu mazan suna da mako ba sa san matan su san suna da kudi, wasu a cewar su wai in kace wa mace kana da kudi mace a lokacin za ta ce muna bukatar abu ka-za da abu ka-za, shi ya sa ba sa fadi amma ai ba uziri bane. Kalubale na farko shi ne; in har matar da ka ke aure ba za ka iya daukar nauyin ta ba shi ne za ka aje ta dauka tunda ba ka iya badawa. Shawara ta ga maza masu irin wanan hali gaskiya ku farga ku gane irin wanan hali ba shi da kyau, Allah ya shige mana gaba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Ma'aurata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Next Post

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Related

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo
Taskira

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo

1 month ago
Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

1 month ago
Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

1 month ago
Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
Taskira

Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu

2 months ago
Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?
Taskira

Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?

3 months ago
Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
Taskira

Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma

3 months ago
Next Post
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

LABARAI MASU NASABA

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

July 5, 2025
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

July 5, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

July 5, 2025
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

July 5, 2025
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

July 5, 2025
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

July 5, 2025
Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

July 5, 2025
Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

July 5, 2025
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (5)

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (5)

July 5, 2025
ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.