Shafin TASKIRA shafi ne daya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma. A yau shafin namu na tafe da wasa-kwakwalwa, inda maudu’in ya fara da cewa;
“Saurayi da budurwa ne suke soyayya, sai saurayin ba shi da kuɗin siyen fili, ita kuma budurwar tana da fili, saboda tsananin son da take yi masa sai ta bashi dama ya je ya fara gini a filinta.
Bayan sun yi aure sun haifafa sai saɓani ya shiga tsakani, suka fara rikici har ta kai ga sun rabu da juna. Shi kuma bai yi dabarar siyan wani filin ya yi gini ba, sai ta ce ita ainihin filinta take so
bata buƙatar gidan ya ɗauke ginin gidanshi ya tafi da shi, ai dama filin nata ne. Shi kuma ya ce ginin gidansa yake so kuma ba wanda zai rushe masa abinsa yana son gininsa a haka”. To, Idan kai ne mijin/ko ke ce matar ya za ku yi? Ga dai bayanan ma’abota shafin TASKIRA kamar haka:
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:

To, wannan matsala dai mai sauƙi ce, saboda akwai ‘ya’ya a tsakanin su, dama kuma haƙƙin iyaye ne su samar wa iyalinsu muhallin da za su zauna cikin rufin asiri. Kuma babu yadda za a yi a raba fili da gidan da aka riga aka gina. Dole ne ɗɗya ya haƙura da wani abu daga ɓangaren sa. Don haka idan ni ne zan mallakawa yaran da muka haifa da ita ne gidan, in ya so tana iya bar musu har da filinta, ko kuma ta yi musu kuɗin fili a biya ta. Tunda fushinta akan mijinta ne, ba za ta yi rigima da ‘ya’yan cikinta ba. Ni ma kuma saboda albarkacin ‘ya’yan ba zan so mu samu rikicin da zai raba kan ‘ya’yana ba.
Sunana Princess Fatima Zahra Mazadu, Gomben Najeriya:

Haƙuri za mu yi kawai mu sauke girman kai, saboda saki ya shiga tsakani, mai fili dole dai filin gida zai dawo, kan ta zauna ko ta rakuɓe. Haka shi ma ba a gini sai da fili in mai fili bai baka fili ba babu ta inda za ka sami damar ginawa har ka zauna. Ni a ganina kawai in ba zai maidata ba ya fanshi filin ko ta fanshi gidan, faƙat! magana ta ƙare.
Sunana Sa’idu Haruna Kunya:

To, a nawa ganin gaskiya mijin ne zai haƙura ya rushe ginin ya bata gunta, tunda ta yi masa halacci tun farko. Ita kuma sai ta yi masa ihsani na ɗan wani abu da zai cika ya sayi wani.
Sunana Aminu Ilyas Isah (Farfesa), Jihar Kano:

Idan ni ne mijin siye filin nata zan yi, in kuma bata yarda ba sai mu je Kotu ta raba mana gardama.
Sunana Hassana Sulaiman, Haɗejia, Jihar Jigawa.

To faa, ai kusan batun nan zan iya cewa ya zo da ‘yar cakwakiya cikinsa, saboda kowa cikinsu a nawa mahangar yana da hujja tare da kuma dalilinsa na buƙatar abin sa yadda ya san shi a baya . Kuma idan ni ce matar a wannan halin sai dai dole tasa na haƙura da filin nawa, na dubi alaƙar dake tsakaninmu ta tsawon zaman da muka yi tare kuma na sake duba ‘ya’yan dake tsakani na haƙura na bar masa ginin gidan nasa, in ya so na siye ginin da yayi mu zauna ni da yaran nawa. Hakan ina ga shi ne mafita musamman a waje na na mace, saboda in da za a ce nayi wani ginin an haɗa ni da aiki ehmn.
Sunana Usman Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

Abu mafi a”ala a nan shi ne, da farko sasanto za a fara nema a tsakaninsu, idan har sasanto ya samu shikkenan idan kuma bai samu ba shi ne ainashin filin za a yi wa kuɗi shi ma sai ayi kiyasi wato kintatar kuɗin daya kashe a wannan ginin. Sai ita matar ta biya wannan kuɗin da aka yi kintata ya kashe tunda ita ta fara nema a bata filinta, idan kuma ta ce ba haka ba sai a yi masa kuɗin wannan filin ya biya ta, wannan shi ne mafita.
Sunana Anas Bin Malik Achilafiya, Yankwashi, A Jihar Jigawa:
A gaskiya idan ni ne mijin matar nan, wallahi ko ɓata lokaci babu, zan haƙura da gidan nan, na mallaka mata, duba da irin halaccin da ta yi min a baya. Domin ba kowace mace ce za ta iya yi maka irin wannan halaccin da ta yi maka ba, koda kuwa ba ni da wani gidan, to zan je na san yadda na yi, na samu mafaka, daga nan sai na samu na sake wani. Da yake su mata suna da tausayi, wataƙila ma idan ta ga na ɗauki wannan matakin, ta zubar da makaman yaƙinta ta yafe min, mu dawo mu jone abinmu, kowa ma ya huta, da wasa kwakwalwarsa.
Sunana Aliyu Idris Jigawa:

Lalle kam, ai shi so haka yake tamkar gamon jini ne. A wani ɓangaren yana iya samar da alkhairi ta fuskoki da dama sai daga ƙarshe kuma ya samar da shiri, ko kuma cutarwa ta shiga cikinsa ta zauna. Ana iya samun ƙalubale a tsakanin masoya ta kowacce fuska, masoyi ya kamata ya yi nazarin cewa ba a dogaro da kayan aro, musamman na matarka, domin duk lokacin da wata matsala ta shiga tsakani dole wani ya yi wa wani gori, domin komai daren daɗewa mai guri zai zo kuma dole mai tabarma ya naɗe.
Mutane Biyar Ke Da Haƙƙin Kula Da Sallar Ƙananan Yara
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi mai albarka.
A wannan lokaci zan ɗan yi jan hankali ga wasu ɓangarori guda biyu kamar haka;
1 – Uba: Tunda shi ne magidanci kuma shi ne wanda sitiyarin kula da gida yake hannunsa.
2 – Uwa: Wacce ita ce da tarbiyyar yaro kusan kashi saba’in kenan, tunda shi uba fita yake yi.
3 – Malamai: Tunda su ne da alhaki na kula da ilimi da koyar da ‘ya’ya bayan iyaye.
4 – Mutanen Unguwa: Su ne wanda tarbiyyar al’umma kacokan take hannunsu.
5 – Jagora: Wanda Allah ya bawa jagoranci kamar; shugabanni ko kuma yayye na gida, wanda su ne idonsu akan dukkanin abubuwan da suke faruwa, kuma su ake kawo wa ƙorafe-ƙorafen abubuwan da suke faruwa.
Zan tafi kai tsaye kan gundarin maganar da nake so nayi wato, abin da Allah (SWT) ya halicce mu akan mu yi, wanda idan bawa ya koma gare shi aka zo tambayar ayyukansa, abin da za a fara tambaya kenan sallah. Magana ta gaskiya akwai gyararraki akan sallah sosai, wanda waɗannan mutane guda biyar dana lissafo ya kamata kacokan gabaɗaya su kalli rayuwar akan sallah.
Shi Uba da matar da ‘ya’yan a ƙarƙashin ikonsa suke, ya kamata su tabbatar da ana yin sallah daidai, kuma ana yinta a kan lokaci. Domin duk ranar da bawa ya koma ga mahalicci aka zo tambayar ayyuka, sallah ake fara kalla. Ko laifuka ne suka yi yawa yaro ya fiya ɓarna, a saka shi ya riƙa yin sallah akan jam’i in Allah ya yarda zai daina.
Uwa ya kamata ta tabbatar da ‘ya’yanta basa yin wasa da sallah, dole ne wannan uwa ta matsa akan wannan, idan lokacin sallah ya yi lallai yaro ya yi Alwala a yi sallah a tafi masallaci.
Malamai idan na zo kansu dole su mayar da hankaki su ajjiye maganganu na siyasa ko na bambancin ƙungiyoyi, su mayar da hankali akan karatun sallar da kuma sallar da ɗalibai za su yi. Saboda malamai su ne magada Annabawa, su za su ɗora yara akan tarbiyya ta addini, kuma su za su koyar da su sallah da karatu.
Mutanen Unguwa dole ne ko kana so ko baka so sai an dawo kamar ‘da’, tunda ‘da’ idan maƙoci za shi masallaci ya ga yara suna wasa zai kaɗa su sai an tafi masallacin nan da su. Kar mu ce ai ba ɗana bane ko ba ɗanka bane, A’a! dole mu komo irin wannan tunda wannan lokacin an fi samun tarbiyya an fi samun abubuwa da yawa. To, dole mu matsa kuma mu tabbata ana gyara masallacin kuma ana yin abin da ya kamata na sallah.
Idan na zo kan shugabanni da yayye na unguwa, za a ga mutun ‘wa’ ne ko kuma babba ne a unguwa amma yana kallon irin abubuwan da suke faruwa na rashin yin sallah na yara, ko ƙannensa ba su damu da yin sallah akan lokaci ba ko yin sallah. To, magana ta gaskiya mu kalli sallah ita ce cikon addini, duk musuluncinka in baka sallah kai ba musulmi bane ba. To, mu tsaya mu gyara sallah, malaman mu da suke ta maganganu akan social media da malamai da suke bayar da magunguna, da addu’o’i akan social media a zo a kalli sallah tun daga kan alwala zuwa tada iƙama, zuwa ruku’u zuwa sujjada, zuwa zaman tahiyya, zuwa sallama, a kalli wannan a gyara.
Wallahi idan muka gyara sallolin mu to, al’amuranmu na rayuwa ma sai sun gyaru, amma ta ya ya za mu gyara, waɗannan mutum biyar ɗin dana lissafo dole sai sun yi aiki akansu. Sannan mu matasa maza da mata mu sani cewar fa dole sai muna yin sallah za mu ga daidai, wasu masifun fa da suke faruwa rashin yin ibadar daidai yadda ya kamata ne. Muna wasa da Sallah, za a samu mutum yana haɗa Azhar da La’asar, yana haɗa magriba da isha’i, haba! minti nawa za ka warewa Allah (SWT) ka gabatar da ibadarka ta sallah, sannan ka ci gaba da harkokinka. “Wa ma kalaƙtal jinnu wal’insu illah liya Abdullah” haka Allah subhanahu wa ta’ala ya faɗa.
To, me ya sa ba za mu ware rayuwar mu kacokan akan yin salloli akan lokaci ba?, Ban da sallah fa in ba azumi da su zakkah ba, babu wani abu da aka ce maka ma yi, duk sauran lokuta an baka dama ka yi neman kuɗinka, ka yi tasbihi, ka yi zikiri, ka yi sadaka, ka yi sauran abubuwa, ka yi zumunci. Amma sallah ita ce aka ce ka yi, sau biyar fa za ka yi ban da nafila, za ka yi Subh za ka yi Zuhr, Asr, za ka yi magrib, za ka yi Isha’i. An baka wannan bonus ɗin ka kasa yin waɗannan guda biyar ɗin a cikin jam’i to, me ka ke yi?, dan me aka halicce ka?.
Ina kira dan Allah mu mayar da hankalinmu wurin yin sallah akan lokaci, kuma yin ta a tsaftace. Tun daga yin alwala cikin nutsuwa, mu yi sallar mu cikin nutsuwa, ka roƙi Allah (SWT) buƙatarka. Iya sallah idan ka riƙe ta, kana yinta yadda ya kamata duk abin da ka roƙa Allah zai baka. Saboda akwai falaloli, akwai ni’imomi a cikin yin sallah da kuma roƙon Allah (SWT). Allah ya sa mu gane, Allah ya sa mu cika da imani, Allah duk wani abu da zai sa mu ga halaka Allah ka nisanta mu da shi, Allah duk wani abu da zai kusanta mu da kai da falallarka da ni’imominka ubangiji Allah ya kusanta mu da shi.
Wassalamu Alaikum.














