Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta karɓi ƙarin buƙatu guda 10 daga ƙungiyoyin da ke neman rijista a matsayin jam’iyyun siyasa, wanda hakan ya kai yawan buƙatun da ke gabanta zuwa 144.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma Shugaban kwamitin bayar da bayani da Ilimantar da masu zaɓe, Sam Olumekun, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis. Ya ce hukumar na nazarin dukkan wasiƙun sha’awa zama jam’iyya da ta karɓa domin tantance waɗanda suka cika sharuɗɗan da za su ba su damar ci gaba zuwa matakin neman rijista.
- INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
- Barau Ya Nisanta Kansa Daga Kiraye-kirayen Ya Zama Mataimakin Tinubu A Zaben 2027
Olumekun ya kuma bayyana cewa adadin mutanen da suka yi rijista a ƙarƙashin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) a jihar Anambra ya kai 168,187. Cikin waɗannan, 97,832 (kashi 58%) mata ne, yayin da 70,355 (kashi 42%) maza ne. Masu shekaru 18 zuwa 34 sun kai 90,763 (kashi 53.97%); ‘yan kasuwa da masu sana’a sun kai 62,157 (kashi 36.92%) sannan ɗalibai sun kai 44,243 (kashi 26.31%).
Dangane da mutane masu buƙata ta musamman (PWDs), 303 (kashi 24.92%) na fama da nakasa ta jiki, sai kuma 207 (kashi 17.02%) Zabiya (albinism). Olumekun ya ce mataki na gaba da hukumar za ta ɗauka shi ne bayyana jerin sunayen sabbin masu rijistar domin bayar da dama ga ‘yan ƙasa su yi iƙirari ko ƙin amincewa da sunaye, domin su ne ainihin masu wannan rijista.
A cewar sa, za a gudanar da wannan aiki ne a dukkan mazabu 326 da ke jihar Anambra daga ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025. Bayan kammala wannan aiki da kuma amfani da na’urar tantance bayyanar mutum ta hanyar fasahar hoto da yatsa (ABIS), za a haɗa sabbin rijistoci da na baya sannan a wallafa su bisa rumfar zabe. Daga nan sai hukumar ta bayyana kwanaki da wuraren da za a fara rabon katin zaɓe na dindindin (PVC) ga sabbin masu rijista da kuma waɗanda suka nemi sauya rumfa ko maye gurbin katin da ya ɓace ko ya lalace.
Olumekun ya ƙara da cewa, katunan zaɓe na rijistar da ta gabata ma za su kasance a shirye don karɓa. Ya ce da saura kwanaki 105 zuwa zaɓe, INEC ta san lokaci ya matse, amma tana tabbatar da cewa sabbin masu rijista a jihar Anambra za su samu damar karɓar katunansu kafin zaɓen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp