Sister Iyami Jalo Turaki
Assalamu alaikum iyaye fatan mun tashi lafiya, barkanmu da sake saduwa a cikin filinmu mai farin jini da albarka na Raino Da Tarbiyya. Yau filin zai yi tsokaci ne a kan kula da muamalar yaranmu.
A yanzu zamani ya zo da wani sabon salo na ruguza tarbiyyar yara da sunan wayewa, ta inda zaka ga mace tana abota da namiji suna muamala tamkar kawaye, Wanda hakan ba daidai ba ne shaidanci ne da lalacewa. A lokuta da dama kafin iyaye su ankara tarbiyya ya gama lalacewa.
Iyaye mu saka ido da wasa kar mu kyale yarinya ta zama abokiyar wani, ko yaro ya zama abokin wata wannan ya saba wa al’adarmu.
Ko a makaranta ko gida ko cikin unguwa kada mu bada kofar yin hakan ga yaro mace ko namiji. Lalacewar zamani ta kai ana tsoro da taka tsantsan a wurin abotar jinsi daya ballantana kuma abotar da ba jinsi daya ba. Matasa da yawa sun lalace ta dalilin wannnan abota da zamani yazo mana da shi.
Mu sa ido sosai wurin ganin da su waye yaranmu ke muamala, mu tabbatar jinsi guda ne abokan huldarsu, a nan ma mu saka ido wurin ganin me suke yi na yau da kullum. Sannan kuma mu kara da addua. Allah ya yi mana jagora.