Daga dukkan alamu akwai wani shiri na musamman daga wasu makiya tsarin dimukradiyya na ganin sun yi wa kokarin Hukumar Zabe INEC na gudanar da sahihin zabe zagon kasa.
Hare-haren ban takaici da ake kai wa ofishoshin hukumar a sassan kasar a ‘yan wattanin nan alamu ne da ke nuni da yin hakan.
- Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Warware Rikici Cikin Lumana Ta Hanyarta
A makon da ya gabata ne, wasu da ba a kai ga gane ko su wanene ba su ka kai hari tare da kone ofishin INEC a Jihar Ogun bayan sun fi karfin masu gadin ofishin. Rahottanin sun nuna cewa, an lalata ginin ofishin da wasu kayyakin aiki da suka hada da akwatun zabe 904 gurbin kebewa don kada kuri’a guda 29, amsa kuwa 30 da jakankunan zabe 57 da kuma akwatun samar da 8, sauran sun hada da katin zabe na dindindin 65,699.
Haka kuma Kwamishinan zabe na JIhar Osun, Mutiu Agboke, ya sanar da cewa, an banka wa ofishin hukumar da ke karamar hukumar Ede ta Kudu wuta. Idan kuma za a iya tunawa ‘yan daba sun kona ofishin INEC da ke karamar hukumar Igbo-Eze a Jihar Inugu da ke yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Hukumar ta sanar da cewa, duk da cewa babu wani mutujm da ya rasa ransa amma an lalata akwatun zabe 748, wurin kebewa don kada kuri’a guda 240 kayyakin amfani na ofis duk da kokarin da ofishin kashe gobara na Jihar Inugu daga garin Nsukka suka yi don shawo kan gobarar.
Bayani ya kuma nuna cewa a watan Afrilu na wannan shekarar, ta sanar da cewa, ta yi asarar na’urrar ‘card reader’ da ya fi guda 99,836 a hare-haren da aka kai mata har guda 42 a ofsihoshinta da wadanda aka kai wa ma’aikatan a cikin shekara uku. Hakanan haka a wasu bayanai da INEC ta bayar ta sanar da cewa, ya zuwa watan Mayu na shekarar 2021, an kai mata hare-hare da suka kai 41 a jihohi 14 a fadin tayayyar kasar nan a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021. A shekarar 2019 kawai, hukumar zaben ta fuskanci hare- hare 9 a jihohi 4, a shekarar 2020 kuma ta fuskanci hare hare 21 a jihohi 9 haka kuma a shekarar 2021 an bayar da rahoto 11 a jihohi 7 na tarayyar kasar nan. A rahoton INEC ta bayyana cewa, hare-haren ya kunshi kone-kone da lalata mata kayyaki.
Yadda kone-konen ke kara karuwa akan ofishoshin INEC da kuma mugun nufi wadanda ke kai hare-haren ya fara tayar da hankulan al’ummar kasa har ana tunanin za su iya shafar sahihancin babban zaben shekarar 2023. Ra’ayin wannan jaridar shi ne lallai wadannan hare haren a bayyane yake cewa da gangan ne ake yin su da nufin tsotara wasu al’umma daga kada kuri’a tun ma kafin a fara harkar zaben.
A nasu bangaren, kasashen Birtaniya da Amurka sun nuna damuwarsu ga hare-haren da ake kai wa ofishoshin INEC da yadda ake lalata kayyanin aiki su a fadin tarayyar kasar nan, sun kuma yi gargadin cewa, lallai wannan babbar barazana ce ga zabukkan 2023 kuma barazana ce ga ita kanta harkar dimokradiyya da kanta.
Duk da hukumar bata huta ba wajen ganin ta gudanar da sahihin zabe ta hanyar samar da hanyar aika da sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa da na’urar BIBAS amma wasu ‘yan siyasa sun dukufa wajen yin zargin kara ga wannan shiri na hukumar zaben ta hanyar kai hare-hare a kan kayan aikin hukumar INEC musamman a wuraren da suke ganin basu da magoya baya masu yawa, abokan hamayyar su ne ke da mafi yawn al’ummar da ke a yankin.
Wani karin abin damuwa a nan kuma shi ne mastalar tsaron da ake fuskanta a wasu sassan kasar nan. Muna daukar wadannan matsalolin guda biyu a matsayin abubuwan da za su iya shafar yadda za a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankalin a 2023.
Tuni rahoto ya nuna cewa, akwai wasu al’umma fiye da 686 da suke karkashin ikon ‘yanbindga. Idan za a iya tunawa a watan Yuni na wananan shekarar ne, kungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru suka haramta harkokin siyasa a masarautar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. Haka kuma matsalar a yankin Arewancin Nijeriya ya tarwatsa miliyoyin al’umma da gidajensu na gado. Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da samar da tsaro daga nan zuwa ranar 31 ga watan Disamba. Muna fatar Allah ya basu nasarar samar da cikakken zaman lafiya.
Tabbas mun ji dadin yadda aka samar da karin matakan tsaro a ofishishin INEC a sassan Nijeriya don kare aukuwar karin hare-haren ake yi.
Bayani ya nuna cewa, an samar da jami’an ‘yansanda, sojoji, DSS da jami’an hukumar kashe gobara don kare ofishoshin na INEC a sassan Nijeriya. Haka kuma Babban Sufeton ‘Yansanda, Usman Alkali, ya umarci Kwamishinonin ‘yansanda su samar da shirin tsaro na musamman don kare ofishoshin INEC a fadin tarayyar kasar nan.
A kan wadannan matsololin muke kira ga jami’an tsaro tabbatar da kamawa tare da hukunta dukkan wadanda aka samu da aikata laifin kai hari ofishoshin hukumar zabe ta INEC. Tabbas masu kai hare-haren nan ba aljannu ba ne. Yakamata a tona masu asiri a kuma hukunta su. Sun cigaba da kai hare-haren ne don babu wanda aka kama aka kuma hukunta. A ra’ayinmu in har aka kai ga kama ‘yansiyasar da ke daukar nauyin masu kai hare-haren tare da hukunta su, to zai taimaka wajen rage hare-haren da ake kaiwa.
A matsayinmu na gidan jarida, muna tsaye a kan bukatar gudanar da sahihin zabe, fatanmu shi ne tabbatar da ra’ayin al’umma ce ke yin galaba a zabukkan da za a gudanar. A ra’ayinmmu kuma daya daga cikin hanyoyin da za a iya cimma wannan burin shi ne tabbatar da cikakken tsaro ga ma’aikata da dukkan kayyakin zabe da INEC ta tanada.