Da akwai bukatar sai ‘yan siyasa sun kai zuciyarsu nesa wajen barin yin amfani da kalaman da ba su dace ba, lokacin da suka je yakin neman zabe.
Irin hakan shi ne yake harzuka zuciyar magoya wani dan takara, bayan wasu na wani dan takarar sun furta kalaman da ba su dace ba.
- Ranar Abokan Hulɗa: NIS Ta Karrama Jami’anta Masu Aiki Tuƙuru
- Za Mu Yi Nazarin Hukuncin Kotun Daukaka Kara – ASUU
Wannan an fi samun hakan ne idan ‘yan takarar mukami daya suka zo yin kamfen a garin dan takarar da yake adawa ba domin komai ba, sai saboda duk mukami daya suke nema, amma jam’iyyun da suke matakara sun bambanta. Bugu da kari kuma idan suna takarar kujera daya kamar dai yadda na fara yin bayani nan nema abin aka fi samun matsala, a irin wannan yanayi, amma kuma wannan idan duk an kai zuciya nesa ba wani abu ba ne.
Allah ai shi ke ba da mulki ga wanda ya so don haka komai nacin mutum duk wadansu hanyoyin da zai bi domin yin hakan, idan lokacin shi bai yi babu yadda zai yi.‘Yan takarar mukaman siyasa daban- daban ya dace su sanc ewa duk wani abin da ya faru ko na kirki ko akasin haka, lokacin yakin neman zabe, ana ta’allaka irin hakan ne da cewa sune sanadiyar faruwar al’amarin na tashin hankali.
Domin kuwa wani dan takarar ma tsoro yake da shakkun zuwa wurin da ya dace ya je yakin neman zaben, ba domin komai ba sai don gudun abinda zai iya faruwa.
Ko da yake dai ba a taru aka zama daya ba, sai dai kuma wani al’amari ba a rasa nono a riga.
Wasu daga cikin ‘yan takarari dan za su tafi kamfen wani gari, ba suyin taka- tsantsan da irin kalaman da suka dace su yi. Amma duk da sanin cewar kalaman batanci lokacin yakinn eman zabe ba su kamata, sai dai kuma wasu ‘yan siyasar harshirin yin hakan suke yi.
Sunaganin tamkar yin hakan zai kara masu wani kwarjini daga wurin jama’a. Ranar Laraba ta wannan makon ce aka fara gangami na kamfen din siyasa inda akes a ran dukkan ‘yan takarar Shugaban kasa 18, za su shigayin kamfen din.
Haka nan ma ‘yan takarar majalisu nDattawa da na Tarayya, duk cikin wannan watan ne za su fara. Masu takarar gwamna da ‘yan majalisar Jiha su sai 10 gawatan Oktoba 2022.
Wannan shi yasa hukumomi wadanda suka hada da hukumar zabe mai zaman kanta, hukumar kula da harkokin gidajen yada labarai da suka shafi Talabijin da Rediyo, cibiyar horar da ‘yan majalisa ta kasa.
Duk dai maganar daya ce ta yin nesa nesa da kalaman batanci irin wadanda ka iya harzuka magoyabaya, su kai garungumar tashin hankali, wanda ba shi ne ake bukata ba a wannan lokaci da ake fama da tabarbarewar tsaro.
Ita ma majalisar zaman lafiya ta kasa karkashin Shugabancin tsohon Shugaban kasa na mulkin soja ritaya Janar Abdulsalam Abubukar tare da wasu mashahuran mutaned a suka hada da Alhaji Aliko Dangote Bishop Hassan Kuka ba a bar ta a baya ba wajen yin hakan. Saboda kuwa za su yi taro ranar Alhamis duk da zummar jawo hankalin ‘yan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki, ganin an fara yakin neman zabe a guiji furta kalaman da ba su kamata.