A ranar Laraba ne, daukacin al’ummar kasar nan da ma na duniya baki daya suka gudanar da Maulidi, domin tunawa da ranar da aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).
A kowacce ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal bayan shekare hijira, Musulman duniya baki daya suna gudanar da bukukuwa, domin girmama ranar da aka haifi Manzon Allah. Wanda a Nijeriya da sauran kasashe gwamnatoci suke bayar da hutu ga ma’aikata wajen gudanar da murna tare da halartar biki a wurare daban-daban kamar a makarantu da cibiyoyi da dai sauran.
- Babu Wata Yarjejeniya Tsakaninmu Da Gwamnatin Tarayya Kan Dakatar Da Yajin Aiki – NLC
- Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a
A bikin Maulidin bana kamar yadda aka saba, shugabanni sun taya daukacin al’ummar Musulmi murna tare da kira a garesu da su yi koyi da dabi’un Ma’aiki, sannan ku yi wa kasa addu’a.
- Maulidin Abuja Kullum Kara Bunkasa Yake-Abubakar Rijana
A ranar Larabar da ta gabata aka gudanar da bikin Mauludi domin murnar tunawa da zagayowar ranar da aka haifi Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam kamar yadda aka saba yi a duk shekara a fadin duniya baki daya, karkashin jagorancin Darikun Sufaye.
A nan Abuja kuma, Kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam, ita ce take daukar nauyin gudanar da wannan muhimmin al’amari, inda taron yake karbar bakoncin manyan malamai daga ko ina a fadin kasar nan, karkashin jagorancin Babban Kwamandan kungiyar na Babban Birnin Tarayya, Alhaji Abubakar Aliyu Rijana.
Kamar yadda aka saba a duk shekara ana gudanar da Mauludin a tsohon filin faretin sojoji na kasa wato ‘Old Parade Ground’, to a wannan shekara ma a can aka gabatar, inda dubban ‘Yan Kungiyar Munazzamatu Fityanun Islam da dimbin makarantun Islamiyya da dalibansu da malamansu da sauran masoya shugaban halitta suka yi dandazo a filin.
An dai gabatar da karatuttuka na Alkur’ani, Hadisai, tarhihin shugaban halitta, kasidu, da zikiran daga bakin malamai daban-daban, sannan an gabatar da bayanai da suka hada da nasihohi, wa’azi da sauran abubuwan da za su amfanar da mahalarta taron.
Da yake zantawa da wakilin LEADERSHIP Hausa a wurin taron Mauludin, Babban Kwamandan na FCT, Alhaji Abubakar Aliyu Rijana, ya fara ne ga gode wa Allah ya yi da ya sake nuna wa al’umma wannan rana mai girma da tarihi. Ya ce babu abin da Musulmi za su yi a duk inda suke a fadin duniya illa, su girmama wannan rana.
“Idan muka dubi girman wannan rana za mu ga ba Dan’adam ba, ba aljanu ba hatta dabbobi tarihi ya nuna mana sun yi murna da ita wannan ta haihuwar shugaban halitta. Sannan da zarar mun ji an ce wannan wata ya kama, to yawaita ayyuka na alheri gami da yafe wa juna,” in ji shi.
Kazalika, ya yi kira ga ‘yan’uwa Musulmi da su za ma masu hadin kai da soyayyar juna a kowane yanayi suka tsinci kansu, inda ya ce ita wannan kungiya ce da take kira musamman domin hadi kan al’ummar Musulmi a duk inda suke a fadin duniya.
A shekara da ta gabata a yayin da ake gudanar da Mauludin an rika samun yara mata suna suma saboda tsananin zafi, wanda a wannan shekara ba a samu hakan ba. Hakan ta sa wakilinmu ya yi masa tambaya cewa kan yadda a wannan shekara ba a samu irin wannan yanayi ba, sai ya ce, “Kamar mutum ne yake tafiya sai ya yi tuntube da wani abu, to ka ga bai kamata a karo na biyu ya sake yin wannan tuntuben ba.
“Alhamdu lillahi, a shekarar da ta gabata shi ma ba wani matsatsi ba ne, yanayin zafi da kuma cunkoson jama’a shi ya haifar da wannan lamari, to sai ya zama bana mun dauki mataki na kiyaye wannan cunkoso da ake samu, musamman kwamitinmu na da ke kula da fannin lafiya sun yi kokari sosai wajen kai-kawo domin dakile faruwar hakan,” in ji shi.
A fannin ci gaba kuwa, Kwamandan ya ce, “A wannan shekara ko da ba mu ce komai ba idanku ya gane muku irin ci gaban da aka samu, domin a shekarar da ta gabata akwai kungiyoyin da ba su samu halartar wannan Mauludi ba, amma a wannan shekara su samu ikon zuwa, sannan mun samu karin al’ummar da suka halarci wannan Mauludi mai albarka. Saboda haka an samu sosai, domin in ka kula mu kanmu ‘yan agajin abin har nema yake ya fi karfinmu, saboda taron jama’a, kuma an fara zagayen na tun daga karfe 8:30 na safe, amma har yanzu kusan karfe biyu wasu ba su karaso ba.
“To babu abin da za mu cewa Allah sai godiya, kuma muna mika godiyarmu gareku ‘yan jaridu, musamman ku LEADERSHIP Hausa da muka dade muna tare, da sauran ‘yan jaridun da suka samu damar halartar wannan Mauludi mai albarka, Allah ya saka muku da alheri ya mayar da kowa gidansa lafiya.”
- Mataimakin Gwamnan Kano Ya Bukaci Musulmi Su Yi Koyi Da Halayen Annabi
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya taya al’ummar Musulmi a Jihar Kano da kasa baki daya bisa murnar bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
A cewar Gwarzo, bikin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen hallita (SAW) na tabbatar da tunawa da kyawawan halayensa tare da jadadda soyayya gareshi.
Mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne cikin jawabin da sakataren yada labaransa, Ibrahim Garba Shu’aubu ya raba wa manema labarai a Kano. Ya ce wannan biki na tuna wa al’ummar Musulmi koyarwar addinin Islama da jadadda bukatar zaman lafiya.
Hakazalika, Gwarzo ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi koyi da halayen Ma’aiki, wanda ke tabbatar da hadin kai tare da kyakkyawan fatan alhairi. Saboda haka sai ya bayyana bukatar muhimmancin girmama juna da hakuri kamar yadda Ma’aika ya koyar.
“Kamar yadda muke nuna farin cikin bisa muhimmancin wannan rana, Ina kara kira ga al’ummar Jihar Kano da su yi amfani da wannan rana domin tabbatar da hadin kai, ‘yan uwantaka, girmama juna a tsakanin al’ummarmu daban-daban,” in ji Gwarzo.
Haka kuma ya bukaci al’ummar Musulmi su gudanar da addu’oin dorewar zaman lafiya da ci gaban al’umma tare da fahimtar juna a Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana aniyarsa na jajircewa wajen yin aiki tare da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf don inganta rayuwar al’umma.
- Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya taya daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
A ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ce aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), wacce ta yi daidai da ranar 27 ga watan Satumba, 2023.
Mataimaki na musamman a bangaren yada labarai na gwamna Dauda, Suleman Bala Idiris ne ya bayyana hakan a takardar da ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a ranar Laraba.
Acewarsa, gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika girmama watan Mauludin kuma su dinga dabi’antuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) ta juriya da taimakon juna da kuma hakuri.
Ya kara da cewa, Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara da kasa baki daya.
- Yadda Gwamantin Jigawa Ta Bayar Da Hutun Bikin Mauludi
Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar don su gudanar da bikin Mauludi na shekarar 2023.
Jami’in yada labarai na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Ibrahim ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta labarto cewa shugaban ma’aikatan, Alhaji Muhammad Dagaceri ya ce, gwamnan jihar, Umar Namadi ne ya amince da bayar da hutun.
A cewar sanarwar ta ce, “Ina son in sanar da ke cewa gwamnatin jihar ta ayyana yau ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal bayan shekare hijira ta 1445 wadda ta yi daidai da ranar 28 ga watan Satumbar 2023, a matsayin ranar hutu don yin bikin zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Muhammad (S.A.W). “
Kazalika, sanarwar ta ce Dagaceri ya yi kira ga ma’aikatan da daukacin Muslmin da ke a jihar da su ci gaba da zaman lafiya da juna su kuma gudanar da addu’o’i domin dorewar zaman lafiya da samun ci gaba.
Bugu da kari, sanarwar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da yin addu’o’in samun kariya daga wurin Allah su kuma ci gaba da yi wa shugabannin addu’a don su samu sukunin yin shugabanci nagari.