Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi ba.
Cibiyar ta Tukur Burutai ta haɗa hannu da da kasar Sin domin saukaka aikin tare da kuma inganta yanayin yadda za a gudanar da binciken.
- Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo
- Kingibe Ya Yaba Wa Tsare-tsaren Bunkasa Ilimi Ga Matasa Na Buratai
Babban Manajan Daraktan cibiyar, Moses Ayom, ya bayyana nasarar da kasar Sin ta samu wajen gudanar da irin wannan bincike tare da ƙirƙirar ire-iren waɗannan na’urorin da ababen hawa.
Daga ciki akwai ababen hawa na motoci da suke amfani da lantarki kashi 80% tare da shafe nisan zagon tafiya me nisan Kilomita 500 zuwa 600.