A ranar Juma’a 6 ga watan Satumba 2024 ne Tsohon Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya) CFR, ya jagorancin tawagarsa zuwa Katsina domin ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’Adua mahaifiyar magiyayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.
Janar Buratai (mai ritaya) wanda kuma shi ne Betara na Biu, Garkuwan Keffi, kuma tsohon ambasadan Nijeriya a kasar Benin ya samu tarbar daya daga ‘ya’yan marigayyar, Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua, Matawallen Katsina wanda kuma shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa a kan sojoji da Alhaji Mustapha da kuma Manjo Janar Abubakar Adamu (mai ritaya).
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (4)
- Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai
Janar Buratai ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama ya kuma yi addu’ar Allah ya albarkaci zuriyar da ta bari.
A jawabinsa, Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua ya gode wa Buratai da tawagarsa ya kuma yaba masa a bisa yadda ya tafiyar da harkokin sojojin Nijeriya a zamanin yana shugabantar su, wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da tsaro a wancan lokacin.
Cikin wadannan suka raka Buratai akwai Birgediya Janar SK Usman (mai ritaya) mni da Hon. Alhaji Aminu Balele (Dan Arewa) da kuma Alhaji Ibrahim Danfulani, Sadaukin Garkuwan Keffi.