• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burin Kasar Sin Shi Ne “A Gudu Tare A Tsira Tare”

byCMG Hausa
3 years ago
G20

Yayin da ake ci gaba da gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20, a tsibirin Bali na kasar Indonesia, hankula na karkata ga ganawar da manyan jami’an sassan kasashe daban daban, mahalarta taron za su gudanar.

Cikin irin wadannan ganawa, akwai wadda aka tsara gudanar ta tsakanin ministan wajen kasar Sin Wang Yi, da sakataren wajen Amurka Antony Blinken, a gefen taron mai matukar muhimmanci.

  • Kasar Sin Ta Jaddada Matsayinta Game Da Batutuwan Da Suka Shafi Yankin Taiwan Da Xinjiang

Masharhanta dai na ganin idan har ana son cimma gajiya daga ganawar sassan biyu, to ya zama wajibi bangaren Amurka ya nuna sahihanci, da yin magana daya, ta yadda hakan zai haifar da amincewar juna, da kyautata alakar kasashen 2 yadda ya kamata.

Duk da cewa an kafa kungiyar G20 ne da nufin warware manyan matsalolin tattalin arzikin duniya, kamar daidaita yanayin hada hadar kudade, da dakile sauyin yanayi, da wanzar da ci gaban duniya mai dorewa.

A bangaren Sin da Amurka, akwai karin batutuwa da ya wajaba sassan 2 su kara maida hankali a kan su, musamman ma batun sabanin su game da kare ikon mulkin kai, da tsaro, da harkokin kasuwanci, da kyautata diflomasiyya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Har kullum, manufar kasar Sin ba ta sauyawa, game da burinta na ganin sassan duniya sun yi tafiya tare, domin cimma moriyar juna, da samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

A wannan gaba, fatan da yawa daga masu fashin baki, shi ne yayin ganawar kai tsaye ta wadannan manyan jami’ai biyu, bangaren Amurka zai amince da muradun kasar Sin, na kauracewa tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, musamman ma batun yankin Taiwan, wanda a baya bayan nan Amurkan ke ta aiwatar da wasu matakai, wadanda ba za su haifar da da mai ido ba.

Cikin irin wadanan matakai akwai batun karfafa ayyukan sojinta, da na tattalin arziki, da kawance da kasashen gabashin Asiya, a wani yunkuri na abun da take kira “Dakile fadadar tasirin kasar Sin”.

Don haka dai ana iya cewa, dangantaka tsakanin Amurka da Sin a wannan lokaci, na cikin wani yanayi mai sarkakiya. Duk da cewa jami’an sassan biyu na ganawa, da tattaunawa sa’i sa’i. Burin kowa a yanzu, bai wuce ganin manyan kasashen 2 sun fahimci juna ba.

Kana su kauracewa dukkanin wani nau’i na fito na fito, tare da rungumar matakan da za su amfani al’ummun su da duniya baki daya. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
NNPP Ta Maye Gurbin Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Da Mamba A Yola

NNPP Ta Maye Gurbin Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Da Mamba A Yola

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version